Shawara Ga Matar Aure Akan Wayar Hannu – Dr. Abdallah Gadon kaya
Babban malamin addinin Muslunci wanda yayi fice wajen karatun mata wanda a wannan zamani Allah ya bashi azanci da wayon magana wajen kira da babba murya wajen yiwa samari da yan mata har da uwan yan mata da samari nasiha a ta farkin musulunci.
A yau babban shehin.malam Dr. Abdallah Gadon kaya yazo kan nasiha akan matar aure wanda insha Allah idan anka bi wannan shawara mace to zata iya rika babbar waya batare da mijin ta yana shakku akan ba sosai ga abinda babban shehin malamin ke cewa.
“Dan Allah ina bada bada shawara akan wayar hannu kiyi waya mai kyau mai girma amma kada kiyi wayar da tafi ta mai gidanki tsada inda hali saboda fitina inko tafi ta mai gidanki tsada bance haramun bane amma dan Allah ki daina shiga wuraren da zasu jawo miki mutuwar aure.
Haramun ne ki rinka kulla alaqa da kawayen banza,haramun ne ki kama daukar shawararin kawayen ki na banza sunfi muhimmanci bisa ga na mai gidanki.
“Kuma haramun kulla alaqa da maza da chatting da maza iya kacinki da maza gaisuwa ya gida ya aiki yanzu abin tausayi zakaga wasu matan group din maza tsudum a ciki kuma zatayi bidiyo ta tura ana hira da ita akan abubuwa ko da sunan business koda sunan wata kungiya ko da sunan wani abu ko wani group na dangi a dangin akwai wanda zai aureta.
“Ki daina daukar hoton bidiyon ki kina turawa ko dawa kawarki ne saboda wallahi ana fita da bidiyo ana abunda bai kamata ba, bidiyon za’a iya hadashi da wani abu wani zai iya yimiki sheri ya hada da wani namiji a aikawa maigdanki yawa yawan daukar hoto da mata kuke yi kuyi nesa wallahi.
Idan kinka dauki hoto kinka turawa kawarki wani abu na iya biyowa baya wani da tsafi zai rabamiki aurenki, kuma ki tuna girma na kamaki zaki iya haihuwar yara su girma su tashi su ga waɗannan hotunan wallahi ki tabbatar idan za’a dauki hoton an dauke shi cikin mutunci da daraja,kuma ina bada shawara mutane su guji daukar hoto abubuwan da ke faru da shi da iyalinsa.
Ka tabbatar da indai anka sa camara anka dauki hoto wallahi yau da gobe zai fita, zaka iya yin wani abu abinda ya kamata da matarka yara su dauka a yada wasu sugani suce ashe wane dan iska ne.”