Kannywood
Hotuna : Ali Jita A wajen Aikin Umrah shida Iyalinsa
Masha Allah a wannan shekarar 2022 Fitaccen mawakin nan Ali Isah Jita ya halarci aikin Umrah A kasar saudia Arabia tare da iyalinsa.
Wannan abun akwai matukar sha’awa sosai duba da daman addinin Musulunci addini ne mai tsafta mai son zama lafiya da kyatatawa iyali.
Babu addinin da ya kawo ayiwa a kyautatawa iyali sama da addinin musulunci mawakin ya wallafa sakon godiya ga Ubangiji da ya bashi wannan damar inda yake cewa.
“Alhamdulillahi na samu yin aikin umrah nida iyalina Allah ya karbi ibadarmu Amen.Allah ya albarkaci dukkan musulmi da samu damar ziyarar wanann kasa mai tsarki da kuma kyauwon gaske da tafi ko ina kyau a duniya nan.#Makkah.
Masu sakon addu’a mun isar da sakon ku.”