Hotuna : Shirye-shirye sun kankama: Ado Gwanja na shirin yin wuff da Jaruma Momi Gombe
Ga dukkan alamu, lokacin auren mawaki Ado Gwanja ya matso don da kan shi ya wallafa kyawawan hotunansa a Instagram da jaruma Momi Gombe inda ya rubuta “Time”, wato lokaci.
Ita ma jarumar ta wallafa hotunansu tare inda ta ce “Alhamdulillah”. Nan da ‘yan uwan aikinsa da mutane masu musu fatan alkhairi su ka bazama su na ta kora musu addu’o’i.ko
Sai dai babu wani bayani dangane da lokacin da za a yi auren, amma da alamu lokaci ya matso don jarumai ciki har da Ali Nuhu su na ta yi musu fatan alkhairi.
Idan ba a manta ba, a cikin shekarar nan auren mawakin ya mutu da matarsa Maimunatu wacce ta haifa masa diya daya.
Sai dai tun bayan mutuwar auren ake ta gutsiri-tsoma dangane da yadda Maimuna ta bayyana cewa akwai wadanda ke da hannu a mutuwar aurensu.
Muna yi musu fatan alkhairi.
Ga wallafar daga shafukan dukansu:
https://www.instagram.com/p/CiLM1yWrTlF/?igshid=YmMyMTA2M2Y=
https://www.instagram.com/p/CiLNdkEIUf8/?igshid=YmMyMTA2M2Y=