Uncategorized

BREAKING :Sojojin saman Najeriya sun tsagaita luguden wuta a Sambisa

Rundunar sojojin saman Najeriya sun tsagaita luguden wutan da suke yi kan ‘yan Boko Haram a Dajin Sambisa
– Rundunar sojin ta kira ‘yan ta’addan Boko Haram su sallama
– Shugaban hafsan sojojin saman Kasar ya bayyana haka a Jiya

Rundunar Sojojin saman Najeriya ta tsagaita luguden wutan da take yi a Dajin Sambissa kan ‘yan ta’addan Boko Haram. Makonnin baya dai Sojojin saman Kasar sun shiga babbaka ‘Yan Kungiyar Boko Haram din da suke dajin na Sambisa da ke Borno.
Yanzu haka dai Rundunar Sojojin saman na Najeriya ta tsagaita bude wuta a Dajin da Boko Haram suke. An yi hakan ne domin wadands suka shirya tuba daga cikin ‘yan Boko Haram din su samu suyi hakan.
Shugaban Hafsun Sojojin saman Najeriya Air Marshal Sadiq Abubakar ya fadawa manema labarai haka a Garin Maiduguri. Yace yanzu an takaita luguden wutar da aka dauki lokaci ana yi kan ‘Yan Boko Haram a Dajin Sambisa. Air Marshal Sadiq Abubakar yace ana neman ganin karshen ‘Yan Boko Haram ne a Yankin.
Shugaban Hafsun Sojojin saman Najeriya Air ya bayyana cewa burin su shine kawo zaman lafiya a Yankin Borno da kewaye. Rundunar Sojojin saman na Najeriya ta dauki fiye da mako guda tana zuba luguden wuta a Dajin Sambisa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button