Labarai
WhatsApp na duba yiwuwar barin Najeriya
Advertisment
Mako guda bayan gwamnatin Najeriya ta ci tarar kamfanin Meta, wadanda su ka kirkiri WhatsApp ta Dalar Amurka Miliyan 200 kan karya dokar bin bayanan sirri, kamfanin na Meta ka iya rufe ayyukansa a kasar sakamakon bukatun da hukumomi suke gabatar masa.
Wasu majiyoyi sun shaida cewa kamfanin Meta wanda ke da WhatsApp na duba yiwuwar janyewa daga Najeriya.
Baya ga cin tarar kamfanin, hukumar FCCPC ta kuma umarci WhatsApp ya dena hada bayanan masu amfani da shi da shafin Facebook ba tare da amincewar su ba.
Sannan hukumar ta bukaci WhatsApp ya bayyana bayanan da ya karba daga masu amfani da shi.
Advertisment
PUNCH