Labarai

Wata budurwa ‘yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin masoyin ta mai dauke da cutar kanjamau domin kada a raba su

Wata budurwa ‘yar shekara 15 a yankin  Sualkuchi, da ke birnin Assam na kasar Indiya ta yi wa kanta allurar jinin da ke dauke da cutar kanjamau na saurayinta, a jikinta bisa dalilin zurfafawa, gami da nunasoyayyar gaskiya a gareshi. Shafin Labarunhausa na ruwaito

Yadda budurwar ta hadu da masoyin nata

Rahotanni sun bayyana cewa,  matashiyar ta hadu da saurayin nata ne ta hanyar Facebook. Daga nan sai  ƙaunar  juna ta ƙaru a tsakanin su, a sakamakon hirar da suke yi akai-akai wadda ta sanya suka kara shakuwa, ta yadda suke jin cewa daya bazai iya rayuwa ba idan babu daya.

kanjamau
Wata budurwa ‘yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin masoyin ta mai dauke da cutar kanjamau domin kada a raba su

A cewar gidan talabijin na Kalinga, masoyan sun kasance tare tsawon shekaru uku da suka wuce kafin yarinyar ta dauki wannan matsanancin  matakin.

A can baya budurwar tayi yunkurin guduwa da saurayin

An ruwaito cewa, yarinyar ta kuma yi kokarin guduwa da masoyinta sau da dama a baya,  amma iyayenta  suna dawo da ita gida.Amma wannan danyen aiki da budurwar ta yi a wannan karon sam babu wani daga yan uwan ta ko kewaye da ya taba tsammanin kasancewar sa.

Ta yiwa kanta allurar jini mai cutar kanjamau

Yarinyar ta yi wa kanta allurar jinin da aka dauka daga wurin masoyinta mai cutar kanjamau, ta hanyar amfani da sirinji.Bayan yan uwanta  sun sami labarin wannan lamari mai ban mamaki, sai suka yi karar  masoyin nata a gaban shari’a .

Yanzu haka ‘yan sanda sun tsare saurayin nata,  yayin da ita kuma take  karkashin kulawar likitoci

Bayan bullar  wannan labari, Jama’a sun yi mamakin ganin yadda matasan kasar ke yanke  irin wadannan matakai  da ba su dace ba, gami  da barazana ga rayuwa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button