Labarai
A rana irin ta yauce aka haifi tsohon shugaban kasa, Marigayi Umar Musa ‘Yaradua
Advertisment
A rana irin ta yauce, 16 ga watan Augusta, shekarar 1951 aka haifi tsohon shugaban kasa, marigayi Umar Musa ‘Yaradua.
Shekaru 69 kenan da suka gabata. Ya mulki Najeriya daga shekarar 2007 zuwa 2010. Hutudole ya ruwaito muku cewa kamin zama shugaban kasa, Marigayi ‘Yaradua ya zama gwamnan Katsina daga shekarar 1999 zuwa 2007.
A shakarar 2009 ne aka fitar da tsohon shugaban kasar zuwa kasar Saudiyya inda yayi jinya. An dawo dashi Najeriya a watan Mayu na shekarar 2010 inda aka tabbatar da cewa ya rasu.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Advertisment