Shekara ta 90 amma ban taba saduwa da ko wacce ‘ya mace ba kuma lafiya ta garau nake
Wani dattijo mai shekaru casa’in s duniya, mai suna Baizire Jean Marie, ya bayyana cewa a tsawon rayuwarsa bai taba saduwa da wata mace ba. Shafin Labarunhausa na ruwaito
Ban taba fita daga kauyen mu da sunan bulaguro ba
A cewar mutumin wanda Basarake ne, tun da aka haife shi bai taɓa fita waje daga ƙauyen sa ba, kuma yana fatan ya karasa sauran kwanakin rayuwarsa a kauyen nasu.
Baizire din, ya bayyana cewa yana da matakin karatun firamare amma takaddar satifiket din bata da wani amfani a wurinsa saboda ya kasa samun wani aiki da shi.
Ban taba saduwa da ko wacce ‘ya mace ba kuma lafiya ta lau
Ya bayyana cewa, yana son ya haifi yaro kamar sauran mutane amma ba shi da mata ko budurwa kuma bai taba kwanciya da kowace mace ba.
‘Yan uwan mutumin mai shekaru 90, sun tabbatar da cewa dattijon garau yake, a hankalin sa da jikin sa da kuma tunanin sa, amma ba su san dalilin da ya sa har yanzu bai fara alaka da kowace mace ba.
Sun danganta yanayinsa da matsala ta aljanu, saboda sauran ’yan’uwansa ba haka suke ba