Labarai

Yadda na samu juna biyu na haihu ba tare da saduwa da wani namiji ba -Wata mata

Advertisment

Wata mata ƴar ƙasar Ghana mai suna Aba, tayi iƙirarin cewa ta samu juna biyu sannan ta haihu ba tare da ta sadu da namiji ba.

Shekarar matar huɗu rabon da ta sadu da wani namiji

Da take magana a wata hira da Barima Kaakyire Agyemang a tashar Step 1 TV, Aba tayi iƙirarin cewa bata sadu da wani namiji a tsawon shekaru huɗu da suka wuce.

A cewar ta, lokacin da ta fara jin wani baƙon ciwon ciki da kumburi, ta ɗauka cewa ‘fibroid’ (ƙarin mahaifa) ne.

Bayan taje asibiti, ta bayyana cewa likitoci sun shaida mata cewa tana bukatar ayi mata tiyata domin a cire shi.

Ta ƙara da cewa ta ji bukatar ta turo ƙarin mahaifar ɗin waje saboda hana yi mata tiyata a ciro shi, a mamakin ta, kawai sai jaririn yaro ya sulluɓo.

Tana buƙatar taimako wajen ɗaukar ɗawainiyar yaron

Matar wacce yanzu ta zama sabuwar uwa tana sayar da ruwa a bakin titi, ta kuma bayyana cewa bata da halin da zata ɗauki dawainiyar yaron. Ta kuma bayyyana cewa wata matar wani fasto ce take ɗaukar ɗawainiyar ta da ta jaririn kaɗan-kaɗan yadda zata iya.

©Labarunhausa

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button