Labarai

Tun Bayan Da Mahaifinta Ya Mata Kwal Kobo Kanta Bai Sake Tsiro Da Gashi Ba

Josepha ‘yar shekaru 28 da haihuwa daga kasar Yuganda, tace tana da shekaru 5 a duniya mahaifinta ya aske mata kanta tas, tun daga wannan lokacin gashin ya daina tsira daga jikinta ma gaba daya.

Bayan askin ne sai mahaifinta ya mutu. Ta kuma kamu da matsanaciyar cuta inda tace da kyar ta sha bayan da mahaifiyata ta kashe kudi wajen nemamata lafiya da kuma tsirowan gasu a jikinta musamman na kanta.

Tace wannan matsalar rashin gashi a kanta yasa maza ko kulata basayi, bakin cikin daya kashe mahaifiyata kenan ta koma gaban kakarta da zama.

A nan ne tace tayi sa’a wani makocinsu yace yana sonta zai aureta, har ma ya kawo sadaki saura ayi bukin ne yace ya fasa aurenta ganin yadda ‘yan uwa da abokansa suke kusheta. Inda suka tabbatar masa idan ya aureni haka yaran da zan haifa masa zasu zama. Ya nemi a maida masa sadakinsa.
Hakan ne yasa Josepha ta yanke tsammanin zama babu aure har lokacin da mutuwa zai cimmata.

Da fata matan da Allah Ya albarkacesu da yalwan gasu, su yi maSa godiya. Ga wata mace saboda rashin gashi ta kasa samun mai cewa yana so barema tayi tsammanin aure.

Daga : Abdul Tonga Abdul

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button