Kada Ka Sassauta Dokar Hana Walwala Da Kulle A Dukkannin Fadin Nijeriya, Dakta Gumi Ga Shugaba Buhari
Daga Comr Abba Sani Pantami
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya ce yadda gwamnatin tarayya ta dauki mataki a kan annobar corona bai dace ba.
Gumi kwararren likita ne wanda ya samu tattaunawa da jaridar New Telegraph a kan yadda shugaba Buhari ke kokarin sassauta dokar hana zirga-zirga a kasar nan.
An fara tambayar malamin ko akwai abinda zai ce ga wadandaa basu yadda da wanzuwar kwayar cutar ba.
Malamin ya bayyana cewa an taba irin wannan annobar a 1918 har zuwa 1920. Za a iya cewa wani karni ne ya juya don haka wata annobar ta samu duniya.
Shehin malamin ya bayyana cewa dole za a samu mace-mace amma akwai matukar amfani idan aka mutunta rayukan kowanne mutum.
Kowanne rai na da amfani don haka ya kamata a kiyayesu ta hanyar rashin sassauta dokar. Yace kullen zai fi inganci sannan a yi addu’ar samun riga-kafi ko kuma maganin cutar kacokan ko kuma duka biyun.
Yace kullen zai fi inganci sannan a yi addu’ar samun riga-kafi ko kuma maganin cutar kacokan ko kuma duka biyun. “Kowacce rai tana da muhimmanci kuma ya kamata ta samu ta tsira.
Ka duba yadda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya rasu sakamakon cutar, Babu wanda yake da tabbacin tsallake wannan annobar.
Duk wani tunanin cewa an kawo cutar ne don rage yawan wata kabila ko addini, ba gaskiya bane,” malamin yace. Kamar yadda ya bayyana, kasa mai tsari za ta iya shawo kan wannan matsalar cikin kankanin lokaci.