Hausa Musics

MUSIC : Zugson – Ni da ke mun dace

MUSIC : Zugson - Ni da ke mun dace

Waka ce na yi ta soyayya, amma fa sabun shiga ne abina, ba wani salo, kidan ma ba wani mai zaki bane. Kuma lokacin da na yi wakar muryata a murance take.

Hakikanin gaskiya yadda suka min kidan wakar nan bai yi min ba, ko-da-ya-ke ba yadda na iya, hakan ya sa na ga ya dace na kokarta na je studio na rera ta biyu.

Ga Kadan Daga Baitukan Wakar:

Ni da ke mun dace
Ko da ‘yan’uwa sun tace
Zuciya ta nace.

Babu kida mai dadi, kuma da ya ke ni kaina wannan shine farkon rera wakata, ban yi wasu salo ba.

Kai ba ma wannan ya karaci tsiyar ba, ranar sai da ruwa ya ban kashi kafin na isa studio, muryata ta disashe, ina rera waka ina tari ko na ji makogwarona ya saki.

A karshe bayan na gama, ga sakamakon, ita ce wakata ta farko, kuma ita ce wacce na fara ji na tsana. A wurina ba ta yi dadi ba, amma za ku iya saurara domin jiyewa kunnuwanku.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button