Bidiyon Jaruma Umma Shehu Da Diyarta Suna Tikar rawa Ya Haddasa Cece-kuce
Yayin da wannan shakuwa da kusanci nasu ya birge da dama, wasu na ganin sam wannan bata dace da tarbiyar uwa ta gari ba.
Wannan ba shine karo na farko da jama’a ke caccakar jarumar ba a kan irin wadannan halayya nata na son sharholiya da kuma sako yarta a ciki.legit na ruwaito
Hakazalika tana daya daga cikin jarumai mata da ake bibiyar duk wani motsinsu domin ganin sun yi dan kuskure.
Kalli bidiyon a kasa:
l
View this post on Instagram
Martanin mabiya shafin nata
aminusbono ya yi martani:
“Kunyi matukar birgeni idan naga daughter ta da mamanta haka nake ganin su kamar kawaye suyi ta bani dariya cikin farin ciki ina adduar Allah yayi musu Albarka yasanya su cikin Aminci duniya da lahira”
bachob40_227 ya ce:
“Barewa batayi gudu”
alameensanni ya ce:
“Amma dai anji kunya”
harunakolina ya yi martani:
“Yau ga uwar banza a nan”
abdulrashiddanladiabubakar ya ce:
“Girma yayi gaddama”
been_sheikh ya tofa:
“Wannan tarbiya tayi”
outlow_killer_makashi ya ce:
“Ikon ALLAH tweens kenan”
souleymane0_ ya yi martani:
“Kamar ‘ya kamar uwa”