Kannywood

Mansurah ga Tinubu: Zan yi maka kamfen da jinina, kyauta, in ka ceto fasinjojin jirgin kasan Abj-Kd

Bayyanar bidiyon fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane ya tada hankulan ‘yan Najeriya.A sabon bidiyon da suka saki, an ga yadda suke zane jama’ar da ke hannunsu da sanyin safiya inda fasinjojin ke ta kuka cike da ban tausayi.legit na ruwaitoHakan yasa hankulan mutane ya tashi inda ake ta kira ga gwamnati da ta yi gaggawar yin abinda ya dace domin kubutar da jama’ar.

Yanzu Haka Gwamnati Zata Zuba Ido Tana Kallo, Ali Nuhu Ya Yi Martani Kan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa
Ba a bar jaruman Kannywood a baya ba, jarumai irinsu Ali Nuhu da Mansurah Isah sun bayyana tashin hankalinsu.

Wallafar Mansurah Isah ta ja hankalin jama’a inda tayi kira ga ‘dan takara shugabancin kasa na jam’iyya APC, Bola Ahmed Tinubu da yayi wani abu, ita kuma zata masa kamfen.

“Zuwa ga Bola Ahmed Tinubu, Wallah wallahi idan ka taimaka mana aka sako fasinjojin jirgin kasa Abuja Kaduna wadanda aka sace, wallahi zan zabe ka, iyalaina zasu zabe ka, jama’a ta za su zabe ka a yankina, duk wani wanda gidauniya ta taba amfana zai zabe ka. Zan yi maka kamfen da jinina.
“Za ka iya, za ka iya bada kudin da suke bukata. Ka yi amfani da kudin kamfen din ka ka fitar da su, mu kuma zamu yi maka kamfen kyauta,” wallafar ta tace.

 

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Mansurah Isah (@mansurah_isah)

 

 

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Mansurah Isah (@mansurah_isah)

.

 

 

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Mansurah Isah (@mansurah_isah)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button