Labarai

Zagin Annabi: Yan Sanda Sun Bayyana suna da sillar Mutumin Da Aka Kashe Kuma Aka Kona Shi a Abuja Saboda Batanci

Zagin Annabi: Yan Sanda Sun Bayyana Sunan Mutumin Da Aka Kashe Kuma Aka Kona Shi a Abuja Saboda Batanci

Advertisment

Abuja – Rundunar yan sandan Najeriya ta Abuja ta ce tana bincike kan kashe wani mutum da aka yi bisa zargin yin batanci a ranar Asabar a unguwar Lugbe a Abuja. Legit na ruwai

Hakan na zuwa ne a lokacin da rundunar ta gano sunan wanda aka kashe a matsayin Ahmad Usman wanda aka ce dan shekara 30 ne da haihuwa, rahoton The Punch .

Kakakin rundunar, Josephine Adeh, ta tabbatarwa The Punch hakan a ranar Asabar, ta kara da cewa rundunar ta fara bincike a kan lamarin.

Ta ce:

Advertisment

Abubuwa sun koma yadda suke a unguwar yayin da jami’an mu suna cigaba da sa ido da tattara bayanai.
“Ana shawartar mazauna unguwar su cigaba da harkokinsu ba tare da tsoro ba a yayin da bincike ke gudana domin gano gaskiyar abin da ya yi sanadin afkuwar lamarin mara dadi da kuma kama masu hannu a ciki.
“Mun gano cewa wani Ahmad Usman mai shekaru 30 kuma dan vigilante ne a Tippa Garage a Gidajen Gwamnatin Tarayya da ke Lugbe a Abuja ya yi musayar maganganu da wani Mallami wanda kawo yanzu ba a gano sunansa ba.

“Musanyar maganganun da suka yi ta yi zafi har ta kai ga rikici ya barke aka kuma malamin ya tattaro mutane kimanin dari biyu suka kashe Ahmad Usman suka kona shi.”

Yan sandan sun ce bayan samun rahoto, jami’ansu sun isa wurin sun kuma kwantar da tarzomar kafin ta wuce gona da iri.

Kwamishinan yan sanda na Abuja, Babaji Sunday, wanda ya yi magana da wakilin The Punch ya yu gargadin mutane su dena daukan doka a hannunsu.

Ya ce:

Ba mu amince da daukan doka a hannu ba. Dokar Najeriya ya hana hakan kuma za a dauki mataki kan wadanda aka samu da hannu wurin aikata laifin.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button