Labarai
Zamu Daure Duk Wanda Ya Sake Zagin Gwamna,sanata ko Shugaban Kasa
Hukumar lura da kafafen yada labarai a Najeriya NBC, a ranar Alhamis ta ce za ta fara hukunta duk tashar watsa labaran da ta sabawa dokokinta.
Ta gargadi kafafen watsa labarai cewa su fahimci dokoki da ka’idojin sana’ar.
Diraktan hukumar NBC na jihar Legas, Chibuike Ogwumike ya bayyana hakan a takardar da aikewa manema labarai.
Yayin bayyana wani sashen dokokin, Chibuike yace sashe na 3.1 ya bayyana cewa “Babu tashar watsa labaran da aka amince ta baiwa wani dama ingiza mutane zuwa aikata wani laifi, da zai iya kai ga rabuwar kai da kuma wanda ya kunshi kalaman batanci kan wani mutum ko kungiya.”
Sashe na 3.1.19 yace: “Ba’a amince kafar watsa labarai ta watsa sakon da ke cin mutuncin al’adunmu.”
Ya kara da cewa: Sakamakon bincike ya nuna cewa kwanakin nan, wasu kafafen yada labarai sun daina aikinus na tantance kalaman mutanen da suka gayyata shirye-shiryensu inda ake zagin shugabanni da masu mulki a fili.”
“Cin mutuncin shugabanninmu da manyamu da kalaman zagi ya sabawa al’adarmu. Muna ganin girman shugabanninmu kuma hakan ne al’adarmu.”
“Zagi da cin mutuncin shugaban kasa, gwamnoni, yan majalisar da sauran shugabanni ya sabawa al’adarmu.”
‘Za mu daure ka idan ka zagi gwamna, Sanata ko shugaban kasa’
Legithausa ta ruwaitocewa a bangare guda, hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa (NBC) ta ci tarar wani gidan radiyo da ke jihar Legas Naira miliyan biyar.
NBC ta bayyana cewa an ci tarar gidan radiyon mai suna ‘Nigeria Info 99.3FM’ saboda yin amfani da wani shirinsu wajen yada labarai marasa tushe da kan iya haifar da hargitsi da tsana a tsakanin jama’a.
Gidan radiyon ‘Nigeria Info’ ne ya fara yada hirar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Obadiah Mailafia, ya yi zargin cewa wani gwamnan arewa ne ya ke shugabantar kungiyar Boko Haram.
Mailafia ya bayyana cewa daya daga cikin tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram ne ya sanar da shi hakan.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, NBC ta yi Alla-wadai da halayyar rashin kwarewar aiki da gidan radiyon ‘Nigeria Info FM’ ya nuna ta hanyar yada a wani shirinsa mai taken ‘Morning Cros Fire’.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com