Labarai

Wata Tsaleliyar Budurwa Yar Kasar Indiya Za Ta Auri Kanta, An Kammala Tsare Biki

Indiya – Miss Kshamu Bindu, wata matar yar kasar Indiya tana shirin auren kanta a wani biki na gargajiya da za a yi a ranar 11 ga watan Yunin 2022 a wani wurin bauta da ke birnin Vadodara, a yammacin Gujarat, rahoton legit

Za a yi al’adu da aka saba yi kafin aure kamar Haldi (inda ake shafa wa amarya kurkur hade da mai) da sangeet (waka da rawa) a safiyar ranar auren.

Miss Kshama Bindu
Miss Kshama Bindu
Bindu za ta tafi Honey Moon ita kadai bayan daurin aure

Bayan auren za ta tafi hutun masoya wato Honey Moon a Goa inda za ta yi makonni biyu.

Abin da kawai babu a bikin shine ango. Don Miss Bandu tana shirin auren kan ne, wannan shine karo na farko da mace za ta fara auren kanta a Indiya.

“Mutane da dama suna kira na suna fada min cewa ni son kowa ne kin wanda ya rasa,” a cewar daliba yar shekaru 24 mai karanta Sociology kuma marabuciya, ta kara da cewa, “Ina fada musu, na yi sa’an auren kai na.”

Bayan na auri kai na, zan cigaba da rayuwa ina kaunar kai na da kulawa da kai na a cewar Miss Bindu.

‘Sologamy’ bikin aure da aka yi inda mutum zai auri kansa, wani lamari ne da ke bazuwa a kasashen yamma cikin yan shekarun nan amma yanzu ya iso Indiya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button