Labarai

Allahu Akbar: Shekara daya da ta wuce suna cin amarcinsu – matashin yana makokin mutuwar matarsa

Advertisment

Wani dan Najeriya mai suna Mustapha Ahmad Junaid ya koka bayan rasuwar matarsa Fatima Zarah, a ranar da ya kamata su cika shekara daya da aure, dimokuraɗiyyar ta ruwaito.Allahu Akbar: Shekara daya da ta wuce suna cin amarcinsu - matashin yana makokin mutuwar matarsa

Zahra wacce ta rasu da juna biyu a ranar Laraba, 7 ga watan Satumban 2022, bayan watanni 8 da aurensu.

Allahu Akbar: Shekara daya da ta wuce suna cin amarcinsu - matashin yana makokin mutuwar matarsa
Allahu Akbar: Shekara daya da ta wuce suna cin amarcinsu – matashin yana makokin mutuwar matarsa

Mustapha ya auri Zahra ranar 26 ga watan Nuwamban 2021 a Jihar Sokoto. Ya yi wallafa a Twitter ranar 26 ga watan Nuwamban inda yace har yau yana fama da radadin mutuwar Zarah.

Kamar yadda ya wallafa:

Advertisment

Zahra, yau ce ranar da ya kamata aurenmu ya cika shekara daya amma bakya nan. Tun bayan rasuwarki babu ranar da ba na tunaninki.

“A wannan ranar shekarar da ta gabata mu na tare cike da farincikin kasancewa da juna. Lallai mutuwa gaskiya ce, na sani.

“Amma mun rabu cewa da kawar juna. Kin nuna min soyayya tsakani da Allah, amma Allah ya fi son ki kasance da shi. “

“Har yanzu ina tuna lokutan da mu ke tare. Kin kasance mace ta kwarai ga kowa. Na kwashe rayuwa ta ina fatan samun mace ta kwarai.

“Cikin sa’a na same ki. Amma kuma Allah be yi za mu dade tare ba. Ina fatan inda yake ya fi nan. Ina miki fatan Ubangiji ya yafe miki kurakurenki ya kuma ba ki Aljanna mafi daukaka.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button