Addini

Makarantar da dole sai Dalibai sun haddace Alkur’ani Mai Girma da Rubuta shi

Tarihin Assasa Makarantar Darul Furqan
Makarantar DARUL FURQAN ta assasu ne ahannun maulanmu Sheikh Ayyouba Gwani Muhammad Alkaramsami (RTA),tun a shekarar 2007 Acikin mahaifarsa ta NGURU LOCAL GOVERNMENT YOBE STATE bayan tattaunawa tsakanin Malam da Amininsa kuma Maqocinsa MALAM QASIM awata ranar Asabar wanda yayi daidai da 30-6-2007 suka tattauna shida amininsa akan yadda zasuyi subayarda gudummarwasu agurin taimakon Addinin Allah (SWT) dakuma samarda ilimi dawwamamme mai amfani ga al’ummar musulmi,taɓangaren samarda HADDAR AL’QUR’ANI cikin sauqi ga al’ummar Annabi,dakuma karantarda littattafai na addinin musulunci babu dare babu rana,kuma cikin iko da Izza ta Ubangiji anan gurin suka samu matsaya akan zasu buɗe wannan makaranta maisuna

DARUL-FURQAN MODEL TSANGAYA SCHOOL.

An assasa makarantun DARUL FURQAN ne akan abubuwa kamar haka:
Yin karatun Alqur’ani ta sigar rubutawa da haddacewa da allo: Ansamarda wannan hanyar ne domin hakan yana bayarda dama da ikon rubuta Qur’ani da ka, a allo ko atakarda,saɓanin yanda ake yin karatun Alqur’ani tahanyar qoqarin hardacewa abaki kokuma atakarda.
Qur’ani da karantashi da Riwayar Warshu: domin shine yafi daidai da rubutunmu na Warsh a Daularmu ta Kalin Borno da Arewa maso gabar.
yiwa yaro bayanin Alqur’ani tahanyar yin Darasu a allonda yarubuta: Kowane dalibi na makaranta idan yarubuta allo yana kawowa malamin ajinsa allonda yarubuta domin sabun bayani da cire kurakuranda akayi wurin rubuta allon, dakuma koyawa dalibi Alqur’ani a sigarda yake, da koyawa yaro Kalmomi da Ayoyi masu kama da juna, dakuma gayawa yaro sirrukan Alqur’ani awurin karantawa, dakuma koyawa yaro abubuwa masu muhimmanci na Haruffa da Jimla da Mutashabihat dayakamata yakula dasu awurin rubuta kalmomi da ayoyin Alqur’ani, dakuma banbancesu alokacinda ake biyamasa allon
Rubuta Alqur’ani Da ka a allo: Shine Rubuta Alqur’ani bayan yaro ya kammala hardarsa, rubutawa abisa saman zuciya batareda kallon Alqur’ani ko saurarensaba alokacinda dalibi yake rubutawa (SATU),
Rubuta Alkur’ani a Takarda bayan rubutawa da ka a allo (SATU): Dalibi yarubuta Alqur’ani atakarda da ka da zuciya batareda gani ko jin Qur’ani ba, bayan dalibi yayi SATU aqalla sau 2 ko 3.
Waɗannan hanyoyi guda 5 damukebi Manhajin Borno ne, amma mun qara gyara wasu.

Makarantar da dole sai Dalibai sun haddace Alkur'ani Mai Girma da Rubuta shi
Daliban Darul Al-furqan kenan
BANBANCE BANBANCE TSAKANIN MAKARANTUN DARUL FURQAN DA SAURAN TSANGAYU.

Daliban wannan makarantu na Darul Furqan ciki dawajen Nigeria basayin BARA kwata kwata it’s prohibited by the school’s authority,Makaranta ta haramta BARA da ROQO kwata-kwata ba’ayi, saidai duk wanda zaizo daga gidansu zaije da abincinsa na safe dana rana, kokuma iyaye ko yanuwansa sukaimasa idan rana tayi kokuma aba Dalibi kudinda zaisiya abinci yaci idan antashi cin abinci

ƘAYYADE ADADIN ƊALIBAI NAKOWANE AJI:

Kowane Aji adukkanin makarantun Darul Furqan yanada ɗalibai 35- 40, babu wani aji da aka baiwa dama yakeda adadin ɗalibanda sukafi 40.

YIN MANHAJA: Kwamitin Makarantar Darul Furqan sun qirqiri Manhaja da jadawali wanda yake ɗaukeda dukkanin wani bayani na Makarantar Darul Furqan, da jadawalin karatun dalibai da lokutan karatu da dokoki, da tsare-tsare da sauransu.
BANGARORIN KARATU: Bayan Ajujuwan karatun Allo da haddar Qur’ani zalla, Darul Furqan tanada bangarorin Qananan yara (Nursery), da Primary Section, da ɓangaren ƴan boko na Junior& Senior Secondary Classes(waɗanda suka samu hardar Alqur’ani), anayin karatun Boko da Kimiyya akullum.

KUƊIN MAKARANTA (SCHOOL FEES):

Asauran Tsangayoyi Galibi koyarwa free ne , wannan ya sa ɗalibai da iyayensu wasu lokuta basa baiwa abun muhimmanci, suma malamai basa samun sukuni da zaman koyarda yara da dalibai.

BIYAN MALAMAI ALBASHI:

Kwamitin shuwagabanni da masu kula da al’amuran Darul Furqan suna biyan kowane malami Albashi aduk qarshen wata, tindaga Malaman boko da malaman Allo na Kowane mataki, saɓanin wasu makarantun ba’ayin haka.

TAKAITACCEN TARIHIN MAI WANNAN MAKARANTAR DARUL FURQAN

Sheikh Ayyouba Gwani Muhammad Alkaramsami (RTA)
Sheikh Ayyouba Gwani Muhammad Alkaramsami (RTA)

Makarantar DARUL FURQAN ta assasu ne tunfarko ba akan gwamnatiba,ta assasu ne ahannun maulanmu Sheikh Ayyouba Gwani Muhammad Alkaramsami (RTA),tun a shekarar 2007 Amahaifarsa ta NGURU LOCAL GOVERNMENT YOBE STATE bayan tattaunawa tsakanin Malam da Amininsa kuma Maqocinsa MALAM QASIM awata rana mai albarka dayamma suka tattauna shida amininsa akan yadda zasuyi subayarda gudummarwasu agurin taimakon Addinin Allah da Addinin Annabi Muhammadu (SAW),taɓangaren samarda HADDAR AL’QUR’ANI cikin sauqi ga al’ummar Annabi,dakuma karantarda littattafai na addinin musulunci babu dare babu rana,kuma cikin iko da Izza ta Ubangiji anan gurin suka samu matsaya 1 akan zasu buɗe wannan makaranta maisuna DARUL-FURQAN MODEL TSANGAYA SCHOOL.Cikin ikon Allah makarantar Darul Furqan ayanzu tanada branch branch guda 69 aciki da wajen Nigeria.

SAKA LITTATTAFAI IRINSU FIQHU, TAUHID, HADITHI, SIRA, ARABIC, TASAWWUF DA SAURANSU.

Dayawa Tsangaya ba sa koyarda ilimi sai mutum in ya gama hadda yadawo yafara Neman ilmi, wannan ya sa dayawan garada su ka gurbata, wa su ma suke zama yan ta tsine.
RIQE YARA DA KOYARDA SU DAGA SAFE ZUWA YAMMA: Kowane dalibi yana zuwa Makaranta qarfe 7:30am, zaiyita karatu ne babu wasa babu yawo ba shiririta, kuma bazai qara fita daga Makaranta ba sai qarfe 5:30pm
ƊAUKAR MATAKAN TSAFTA MUSAMMAN RANAR ASSEMBLY: Makaranta .

Wannan sune document da zaku iyar saukarwa na tarihin wannan makarantar da wuraren da jahohin da kasashenmu na Afrika da suke da branches na wannan makarantu tare da sunayen malamai da number wayarsu dan karin bayyani.

BABI NA 1

BABI NA 2

DARU Branchess

Majiyarmu ta hausaloaded mun samu zantawa da day daga cikin ɗalibi wanda zamu kira Alaramma Al-Ameen Abdulfattah ya bamu duk wannan tarihin da wannan bayyani da munka kawo muku wanda yana daga cikin daliban din makarantar.

Ga su nan kasa.

Makarantar da dole sai Dalibai sun haddace Alkur'ani Mai Girma da Rubuta shi
Wannan shine kadan daga cikin sashen da Alaramma Al-Ameen Abdulfattah ya rubuta
Makarantar da dole sai Dalibai sun haddace Alkur'ani Mai Girma da Rubuta shi
Certificate na Alaramma Al-Ameen Abdulfattah

 

Makarantar da dole sai Dalibai sun haddace Alkur'ani Mai Girma da Rubuta shi
Alaramma Al-Ameen Abdulfattah
Wanda yayi wannan Rubutu akan Makarantar su

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button