Bayan Maka Miji a Kotu, Matar Aure ta Hana Alkali Raba su, Tana so ya Canza Hali Kawai
Kaduna – Wata matar aure mai suna Bilkisu Muhammad a ranar Litinin ta yi kira ga wata kotun shari’a a Kaduna da kada ta tsinke igiyar aurensu da Sirajo Mansur saboda tana son mijinta ya sauke nauyinta da ke kan shi. Legit na ruwaito
Muhammad ya shigar da karar a ranar 23 ga watan Mayu, inda ya ce ya tafi Legas neman aiki amma ya kasa samar da abinci, wurin zama, tufafi da kudin makarantar ‘ya’yan shi.
Vanguard ta ruwaito, ta bukaci kotu da ta sa Mansur ya biya kudin haya, ya samar da abinci kuma ya biya kudin makaranta.
A martaninsa, Mansur wanda ya samu wakilcin ‘dan uwansa Sulaiman, ya ce wanda ake kara ya umarcesa da ya sanar da kotu cewa ta tsinke igiyar aurensu tunda matarsa ce ta maka shi a gaban kotu.
Ya kara da cewa, ya yi kokarin biyan kudin haya amma mai gidan ya ki karbar kudin saboda ya riga ya bai wa wani dakin.
“A bangaren kudin makaranta, a halin yanzu yara suna rubuta jarabawa ne. Zan biya kudin makaranta bayan an kammala jarabawa,”yace.
Alkali Malam Rilwani Kyaudai, ya umarci wanda ake kara da ya biya kudin haya, ya samar da abinci kuma ya biya kudin makarantar yaran shi.
Ya umarci mai gidan hayan da ya hallara a gaban kotu bayan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Yuni.