Kannywood
An yanka ta tashi : wanda yace zai auri Safara’u yace ko sunanta banson ji – Muhammad T shehu
Advertisment
Idan baku manta ba kwanakin bayyani mun kawo muku rahoton cewa wani matashi mai suna Muhammad t shehu yayi ikirarin auren Safara’u kwana casa’in duk da yadda ta bi duniya.
Wanda Wannan furucin nasa ya jawo cece kuce sosai wanda a rubutunsa ya nuna na Safara’u ake kiransa inda yayi tufka da warwara inda ya sake wallafa rubutu a shafin nasa cewa kusure ne yayi ga abinda yake cewa.
“Jama’a ku shaida, maganar Auren Safara’u wallahi da wasa nake, nayi kuskure !”
Ya kara da cewa
Advertisment
“Dan Allah a daina alakantani da Safara’u, yasin yanzu ko sunan naji an kira sai gabana ya fadi”.
To malam Muhammad T shehu ya raba gari da mawakiya Safara’u tsohuwar jarumar masana’antar kannywood.