Labarai

‘Yan sanda sun kama mijin da ake zargi da kashe mata a Borno

A arewacin najeriya ana samun irin wannan labarun kashe mata ko kashe miji wanda a jihar borno kuma kashe mata da miji keyi wannan shine mummunan labari da ake samu majiyarmu ta samu wannan labari daga wani mutum mai amfani da kafar sada zumunta usman Rabi’u a shafinsa na facebook

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno a ranar Juma’a ta tabbatar da kama wasu mutane biyu, Adamu Ibrahim da Bukar Wadiya bisa zargin kashe wata mata mai suna Fatima Alhaji-Bukar ‘yar shekara 24.

Marigayiyan mazauniyar Dikechiri ne a unguwar Bayan Gidan Dambe a cikin birnin Maiduguri a jihar Borno.

'Yan sanda sun kama mijin da ake zargi da kashe mata a Borno
‘Yan sanda sun kama mijin da ake zargi da kashe mata a Borno

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sandan ysnkin, ASP Sani Kamilu, kuma ya bayyanawa manema labarai a Maiduguri ranar Juma’a.
A cewarsa, marigayiyan tana auren Mista Ibrahim, wanda shi ne babban wanda ake zargi da aikata laifin.

“A ranar 18 ga Oktoba, 2023, wani Adamu Alhaji Ibrahim mai unguwar Dikechiri bayan Gidan Dambe Maiduguri ya je sashin Gwange, tare da wani Bukar Wadiya, ya kai gawar wata mata da ya ce ita matarsa ce, ya kuma nemi agajin gaggawa daga jami’an tsaron ‘yan sanda,” in ji shi.

“Mijin wanda ya yi ikirarin cewa shi ma’aikaci ne a wani banki kasuwanci a Maiduguri, ya dawo daga aiki da misalin karfe 5:00 na yamma. sai ya iske marigayiyar tana kwance a cikin jini.”

A cewarsa, binciken farko da aka yi ya nuna cewa kafin faruwar lamarin, ma’auratan sun samu sabani a cikin gida kan zargin karin aure da mijin ya yi a gidan aurensu.

Ya bayyana cewa an tsare gidan da lamarin ya faru kuma a yayin bincike an gano wasu kayayyaki da suka hada da gajeriyar fulawa guda daya, jaka, igiya, kafet jike da jini, wuka, da motar Honda da tabo

Malam Kamilu ya ce babu wata shaida da ta nuna cewa an karye kofa ko shiga gidan, kuma mijin ne kawai ke da mabudin gidan.

Ya ce mijin da Bukar Wadiya duk an kama su ne a matsayin wadanda ake tuhuma, yana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi domin gurfanar da su gaban kuliya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button