Jiki magayi : karuwai sunyi yiwa direbobi yajin aikin mako 1 jan kunne
Karuwai sun yi wa direbo yajin aikin mako 1 kan cin zarafin abokiyar aikinsu da aka yi
A juma’ar da ta gabata a Nairobi, karuwan yankin Kombosa na kasar Kenya sun hada kai da yan kasar Afirika ta gabas wajen yin bore a kan yadda direbobi ke cin zarafin mata Shugaban kungiyar kare hakkin karuwai ta gargadi mambobin da kin biyawa direbobi bukatar su na tsawon sati daya don nuna bacin ransu A cewarta, hakan ne hanyar neman adalci ga yadda ake cin zarafin mata a bayyanannun wurare da ke birnin
An kama wadanda ake zargin, bayan yawon da bidiyon yadda aka kai hari ga mai korafin yayi a 4 ga watan Maris. Inda aka samu labarin yadda jakadiyar kasar Zimbabwean ta kai kara kofishin yan sanda na Parklands.
Maryline Laini, Daraktan Nkoko Injuu Afrika, kuma CBO dake shugabantar kungiyar kare hakkin karuwai, ta sanar da yadda bisa nuna kauna, mambobin kungiyar bazasu biyawa direbobi bukatar su na tsawon sati daya ba, shafin linda ikeja da legithausa na ruwaito.
Laini ta ce;
“Wadannan mutane kwastomomin mu ne, amma daga yau babu wata karuwa dake da rijista za ta biya wa wani direba bukatar shi a wannan yankin. Idan kuma aka kama wata mamba da wani matukin bodaboda a cikin wannan lokacin, za’a soke rijistar ta” Haka zalika, Laini ta fadawa K24TV yadda suka haramta wa direbobi bukatar su, saboda hakan ne hanyar neman adalci ga matan da ake cin zarafin su a bayyanan nun wurare.
Ta kara da cewa;
“Mun san cewa ta nan ne inda muke samun manyan bukatun mu da daukar ragamar iyalan mu, amma a shirye muka da shan yunwa don kawo karshen irin wannan cin zarafin.”