Uncategorized

Babbar matsalar Kannywood shi ne karancin ilimi a masana’antar, Aminu Shareeff

Fitaccen jarumin Kannywood kuma mai gabatar da shirye-shirye a tashar Arewa 24, Aminu Shariff wanda aka fi sani da Momo ya bayyana babbar matsalar da ta addabi masana’antar Kannywood da kuma hanyar maganceta.

A wata tattaunawa da BBC Hausa tayi da shi a shirin Daga Bakin Mai Ita, ya fara da gabatar da kansa inda yace sunansa Muhammad Al-Amin Aliyu Sharif, inda yace akwai masu yi masa lakabi da sunan Momo da ya fito da shi a cikin fim din Ukuba.

Ya ce an haife shi a Kano, ya yi karatu tun daga firamare har jami’a a Kano inda yayi karatu a jami’ar Bayero da ke Kano, ya yi karamar Diploma, babbar Diploma sai kuma Digiri da sauran takardun ilimi.

Ya ce ya fara shigowa masana’antar ne a matsayin marubuci, sai ya fara shirya shirin sannan daga bisani ya tsinci kansa a matsayin jarumi.

Yayin da aka tambaye shi matsayin mutumin banza ko na arziki, wanne ya fi son fitowa a shirin fim, cewa yayi ko wanne matsayi aka ba shi in har zai isar da sako yana amsa.

A cewarsa, matukar zai burge masu kallo kuma ya nishadantar da su tare da isar da wani sako, tabbas zai tsaya tsayin daka wurin taka rawar da aka ba shi. Jaridar LH na wallafaBabbar matsalar Kannywood shi ne karancin ilimi a masana’antar, Aminu Shareeff

An tambaye shi idan yana fuskantar kalubale daga wurin abokan sana’arsa akan shirin tambayoyi da yake yi musu, cewa yayi ba ya fuskantar wanu kalubale.

Ya ce hasali ma duk wanda aka ga yana shakkar amsa tambayoyin wadanda yawanci akan sana’arsa, wanda ya daga sa ko kuma rayuwarsa to tabbas yana da lam’a.

Kuma ya ce ta yuwu yana tsoron yin karya ne kasancewar akwai wadanda su ke kallon shirin da su ka san shi a waje kuma idan yayi karya sun sani. Don haka in har dai yana da gaskiya bai dace ace sun yi shakka ba.

An tambaye shi hanyar magance matsalar kannywood inda yace:

“Babbar matsalar Kannywood shi ne ilimi, yaduwar ilimi a tsakanin ayyukan da ake gabatarwa da kuma wadanda su ke gabatar da ayyukan. Idan aka samu cikakken ilimin yadda za a gudanar da harkar, mutane za su san me ya kamata su yi, wanne irin sakwanni ya kamata a isar sannan kuma su waye ya cancanta su gabatar.

“Wannan shi ne abinda ya ke damun mu ta hanyar ilimi babu irin nasarar da ba za a samu ba sannan za a dinga yin shirye-shiryen da mutane za su dinga bugun kirji su na alfahari dasu.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button