Abin Kunya Ne Fitowar Wannan Takarda Daga Gwamnatin Nigeria (Karanta wannan abin kunya)
Daga : Attahiru Muhammad marnona
Kamar yadda aka rubuta a wannan takardar gwamnatin Nigeria ta nemi duk wani dan Nigeria dake son ya dawo gida daga Saudi Arabia da ya biya kudi Naira (297,000) a matsayin kudin tsare shi da gwamnati zata yi tsawon kwana 16 kafin ya wuce Garin su.
Wannan takardar cike take da qaranta da rashin tausayi, Muna Kira ga mahukunta da suji tsoron Allah, haka muna Kira ga makusantan Gwamnati da da su sa a janye ta, dama zancen biyan Kudi nan, domin kwata-kwata babu adalci a ciki, kuma girma da mutuncin Nigeria ya wuce ace ta yiwa yan Kasar ta haka, a daidai Lokacin da Kasashe irinsu Saudi Arabia, Malaysia, Kowet, Egypt, suna dawowa da yan Kasar su kyauta ko kudin Air ticket basa biya. Wannan sharadin na biyan Kudi da Nigeria tasa ko Somalia bata sama yan Kasar ta shi ba, bale Babbar Kasa irin Nigeria.
Ko anan Jami’ar da nake ‘yan kasashe da dama sun koma Gida, babu wani Students da ya biya Kasar sa Kudi kafin ya koma Gida, sai gare mu Nigeria za’a fara.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




