APC ta fada tarkon mu ta dauko Tinubu – Reno Omokri
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya maida martani ga tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress a zaben 2023. Jaridar LIB na ruwaito
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, Omokri wanda ke yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP yakin neman zabe, ya ce jam’iyya mai mulki ta fada tarkon su inda ta dauko Tinubu.
Ya yi ikirarin cewa Tinubu ba zai samu kuri’un Arewa da Kiristan Arewa ba kuma ba zai tsira daga tikitin Musulmi da Musulmi ba.
Omokri ya wallafa a shafinsa na Twitter;
Yanzu da APC ta fada tarkon mu ta dauko Tinubu, mun yi matukar farin ciki. Tinubu dan takara ne maras kyau. Amma wannan ba ko kalubale ba ne. Wanene zai zama mataimakinsa? Kiristan Arewa ba zai samu kuri’un Arewa ba. Kuma ba zai iya tsira daga tikitin musulmi da musulmi ba!