Labarai
Shugaba Buhari Ya Ki Ganawa Da Ganduje A Daura
A ranar Asabar din da ta gabata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya watsawa gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kasa a ido sakamakon kin ganawa da ya yi da shi a Daura, kamar yadda majiyarmu ta jaridar DAILY NIGERIAN ta tabbatar.
Ganduje ya yi tattaki takanas ta-Kano ne domin ganawa da Buhari wanda yake hutun mako guda a Daura. Jim kadan bayan bijirewa ganin Ganduje da Buhari ya yi, nan take jami’an tsaro suka nemi tawagar Ganduje su gaggauta barin harabar gidan Shugaba Buhari dake Daura.
Jaridar ta kara da cewa, wannan ya sa Gwamnan cike da takaicin da aka yi masa ya yanke shawarar kai ziyara ga ‘yar Buhari, sannan kuma ya tsaya kallon hawan Daushe a nan Daura.
Sotuces:facebook/rariya
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com