Abun Tausayi : Allahu Akbar Malam Kawu malami Mai Digirin Agricultural Engineering Amma yana sana’ar tura ruwa
A yau din nan ne munka samu wani labarin wani bawan Allah wanda yayi Digirin Agricultural Engineering bai samu aiki ba ya kama sana’ar tura ruwa kamar yadda wani bawan Allah mai suna Ramadan Buba ya wallafa.


Wannan bawan Allah da kuke gani a hoto sunan shi Kawu Malami, dan karamar hukumar Misau ne da ke jahar Bauchi, wanda ke sana’ar tura ruwa a amalake a nan garin Jalingo. Hakika akwai abubuwa masu sosa zuciya a labarin wannan bawan Allah. Mun hadu da shi a bakin kasuwar Jalingo a sana’ar sa ta saida ruwa, inda amalankensa ta mangaji tayar motar wani bawan Allah har tayar ta fashe, ganin yadda ya shiga tashin hankali wannan bawan Allah mai tausayi yace ya yafe masa, zai je ya canja tayar, amma yaje ya nemo masa vulcanizer, take ya nemo aka canja tayar mai motar ya biya har ma ya kara masa da kyautar N500, ganin wannan kyautatawa da mai motar yayi yasa aka fara hira a kan rayuwa, inda a nan muka fahimci ashe wannan mai ruwan graduate ne, Degree yake da shi a Agricultural Engineering.


Da farko mun so muyi tantama a kan hakan, duk da yanayinda kasar nan take ciki mutum kan iya sana’ar yasar shadda ma don ya rufawa kansa asiri, sai dai daidaikun mutane ne zasu iya yin hakan da degree. Da farko kamar ba zamu yarda da zancen sa ba, amma bayan doguwar tattaunawa mun fahimci Kawu gaskiya ya fada, kuma mun bincike shi sosai, ya hadamu da yan garin su da suke tura ruwa tare, da ma ‘yan uwan sa a can gida, inda aka tabbatar mana Kawu mutumin kirki ne, wanda ba karatun boko kawai ba, har na addini yana da shi dai-dai gwargwado, yana kuma da aure har da ‘ya’ya. Daga karshe muka nemi amincewar sa cewa zamu dau hotonsa mu yada ko wani a Bauchi ko wata jahar daban zai taimake sa, kuma ya amince har ya hada mu da ‘dan uwan sa da ya dau hotunan takardunsa ya turo mana.


Abun lura a labarin Kawu shine, duk da shi ba mutum ne mai mutuwar zuciya, da kuma girman kai ba, amma munaga ya cancanci sana’ar da tafi saida ruwa a amalanke, kuma shi kansa yace yaso ace wata sana’ar yake koda tuka Keke Napep, to amma bai samu wannan damar ba, don ba kowa bane zai dau dukiyar sa ya bawa bako. Amma dai gaskiya akwai takaici, kuma ya bayyana akwai dubban mutane kamar shi, amma taimako da tallafawa marasa karfi su tashi yayi karanci a yankin da yafi fama da talauci da rashin abun yi (Arewa). In har Kawu zai iya tura ruwa don ya rufawa kansa asiri, akwai wayanda ba zasu iya ba, sannan a cikin haka ake samun masu sauya tunanin su zuwa aikata laifuka da zasu hana kowa sakat a kasa.
Akwai bukatar gwamnati da masu hanu da shuni su taimaki irin wayan nan, in aiki ya samu fa lillahil hamdu, in kuma jari ne a bawa irin wannan don su tashi. Saboda haka kofa a bude take ga masu niyar taimakawa, musamman a can jahar sa Bauchi inda yace dole ce ta sa shi baro gida, a taimaka masa da jari don ya dogara da kan sa.
Ga lambobin sa da na makusancin sa.
Kawu Malami
08039732142
08084804104
Dan uwan sa!
Al-mansur Muhammad
07038569066
Dan Allah a taimaka a yi share zuwa ga mutane domin taimawaka wannan bawan Allah.