Labarai

Ƙazamin Faɗa tsakanin Yan bindiga : Bello Turji ya kashe Ƙasurgumin Ɗan bindiga Dullun

Abunda Ya Faru Shine Akwai Wasu Ƴan Bindiga ƊAN BOKKOLO Da DOSO Waɗanda Ƙannene Kuma Yaran Ɗan Bindiga Bello TURJI Be Dake Fakai Zaune Dake KWARE a Chikin Ƙaramar Hukumar Mulkin SHINKAFI. Waɗannan Yaran Turji Sunje Yankin BUNGUƊU Da MARADUN Suka Sato Dabbobi Masu Yawa Sosai. Akan Hanyar Dawowa Wadda Tilas Sai Sun Biyo Ta Yankin Jangeru Kudu Ga Garin Shinkafi Wanda Yake Wannan Hanya Ta Biyo BURTALIN ƘAUYEN MANIYA Inda a Nanne Mazamnin Ɗan Bindigar DULLUM. Maniya Ƙarkashin Jangeru Take Amma Tafi Kusa Ga Garin Badarawa.. Basharu Altine Guyawa isa ya wallafa

Nanne Ɗan Bindiga DULLUN Ya Tayasu Kuma Ya Ƙwache Waɗannan Shanu Ya Kashe Wasu Yara Daga Chiki. Shikuma Turji Najin Haka Sai Nan Take Yayo Gayyar Su BOKA Data ATARWATSE Dake KAGARA Da Wani Ɗan Bindiga Da Akechema STANDARD Dake Yankin ZURMI Har BIRNIN MAGAJI, Sukayo Tsinke Saman Mashin Yafi Ɗari Ukku. Kowane Ɗauke Da Mutun Uku Uku Har Maniya…

Nanne Aka Kwashe Tsawon Awa Biyu Zuwa Uku Ana Bata Kashi Da Miyagun Makamai. Akwai Tabbachin Kowane Ɓangare An Jikkata Mutane Waɗanda Allah Kaɗai Yasan Adadinsu.

Akwai Tabbachin Bello TURJI Da Yarashi Gabaɗaya Sun Toye MANIYA Kuma Sunkashe Wannan HATSABIBIN ƊAN BINDIGA DULLUN.. Tare Da Manyan Kwamandodinshi. Majiya Mai Ƙarfi Da Gayamin Chewa Aƙalla Mashin Sabbi Wanɗanda Turji Yasamu Ganima Sunfi Hamsin. Tareda Buhuhuwan Kuɗdi Fiye Da Goma Da Runbunan Abinchi. Irin Shinkafa Da Ababe Da Yawa Waɗanda Akache Shi Kanshi Bello TURJI Yayi Mamaki Matuƙa.

Akwai Tarin Miyagun Makamai Waɗanda Akache Rumbun Makaman Ɗan Bindiga DULLUN Ne Dake Ƙarƙashin Ƙasa. Za’a Iya Tabbatar Da Chewa Dullun Yanada Miyagun Makamai Tun Daga Irin Makamin Da Ake Ganin Shina Ratayawa Ga Wuya Ko Kafaɗa.

Shi Kanshi Bello TURJI Wata Majiya Tache Badon Taron Yawaba Idan Saboda Makamaine Sai Dai Ayi Kwanaki Ana Gumurzu Badon Ya Chanye DULLUM Ba.

Bayan Bello TURJI Yakashe DULLUN Yakame Wasu Yaranshi Tare Da Ƙone Ƙauyen Maniya Kaf. Ya Garzaya Wasu Tungargaki Dake Ƙarƙashin Garin BIRNIN YERO Kusa Ga SHINKAFI Inda Ake Kula Da Dukiyar DULLUN Ta Dabbobi Gaba Ɗaya Ance Ƙauyuka Uku Ne. Suka Ƙone Ƙauyukan Suka Gargaɗa Dukiyar DULLUN Suka Wuce Da Ita Fakai Mazamnin Ɗan Bindiga Bello TURJI.

Akwai Tabbachin Kowane Ɓangare Yasha Wuya Kuma Ankashe Mutane Masu Yawa. Amma Mutane Sun Tabbatar Da Bello TURJI Ya Kwashe Gawar Yaranshi Tare Da Waɗanda Suka Samu Miyagun Rauni. Har Zuwa Wannan Lokachi Akwai Tabbachin Gawar Wakin Dake Chikin Garin MANIYA Harda Ta Dullun Sunanan Fili, Domin Babu Bayanin Hukumomi Sun Shiga Domin Sanin Abunda Ke Chikin Ƙauyen MANIYA Wanda Bello TURJI Yaƙone Ƙurmus Tareda Kashe Dukan Ƴan Bindigar Dake Ciki….

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button