Sheikh Zain Al-Abidin ya zama sabon ma’ajin mukullin Ka’aba
Iyalan Al Shaiba masu alhakin kula da ɗakin Ka’abah sun zaɓi Sheikh Abdul Wahab bin Zain Al-Abidin Al-Shaibi a matsayin wanda zai riƙe makullin ɗakin Ka’aba, bayan mutuwar Sheikh Saleh Al Shaiba a makon da ya gabata.
Sheikh Abdul Wahab, mai shekara 78 shi ne mutum na 110 a jerin magadan Sahabi Uthman bin Talha, wanda ya fara ajiye makullin Ka’abar a zamanin Manzon Allah (S.A.W), kamar yadda shafin Haramain ya ruwaito.
An zaɓi Shehin malamin ne a wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a gaban fitattun mutanen iyalan zuri’ar Al-Shaiba da ke kula da makullin ɗakin.
A lokacin bikin an miƙa makullin a hukumance zuwa hannun Sheikh Abdul Wahab, lamarin da ke alamta karɓar aikin kula da ɗakin mafi tsarki a musulunci.
Iyalan Al-Shaiba sun samu darajar ba su damar kula da ɗakin Ka’abah na tsawon ƙarnuka, aikin da ake kallo a matsayin mai ƙima da daraja a duniyar musulunci.
Yayin da yake jawabi a lokacin bikin, sabon mai kula da Ka’abar ya ce a shirye yake wajen martaba al’adar da aka san zuri’ar Shaiba da ita ta kula da ɗakin.
BBC Hausa