Addini

Sheikh Nuru Khalid ya samu sabon Masallacin da zai ci gaba da limanci

Advertisment

Bayan awanni da kwamitin Masallacin Juma’a na Apo ya sanar da sallamar shi gaba daya, Sheikh Nuru Khalid ya samu wani Masallacin da zai ci gabs da limanci.

Wannan na zuwa ne a ranar da Kwamitin Masallacin na Apo ya sanar da sallamar shi gaba daya, bayan ya dakatar da shi tun da farko.

A karshen makon nan ne dai Kwamitin Masallacin, karkashin Sanata Sa’idu Dansadau ta fitar da sanarwar dakatar da malamin daga limancin saboda hudubarsa ta ranar Juma’a a kan matsalar tsaro.

To sai dai kuma jaridar Aminiya ta rawaito cewa Sheikh Nuru ya ce tuni Kwamitin Gudanarwar sabon Masallacin Juma’ar da aka gina a unguwar ma’aikatan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ba shi limanci a can.

Advertisment

Ya ce zai fara jagorantar sallah ne daga ranar Juma’a, takwas ga watan Afrilun 2022 mai zuwa.

Ya ce, “Da yardar Allah zan fara jan sallah a sabon masallacina ranar Juma’ar nan mai zuwa, saboda a matsayinmu na limamai, dole sai mutum ya samu wajen da zai rika limanci.

“Akwai sabon masallacin da muka gina a bayan unguwar CBN, ni ne zan rika jan sallah a can,” inji shi.

Malamin dai ya bayyana sallamar da aka yi masa daga masallacin na Apo a matsayin kaddararsa, saboda ya fadi gaskiya.

A yayin hudubar tasa dai, malamin ya kalubalanci gwamnati mai ci kan yadda ya ce ta gaza magance matsalar tsaron da ya addabi al’umma, musamman ma a kan harin jirgin kasan da aka kai a tsakanin Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button