Addini

Yadda na haddace Al-Qur’ani tun ina da shekaru 3 a duniya, Dan shekara 8 din da ke tafsiri a Zaria

Ba Qur’ani yake karantarwa ba, har da hadisi da sauran littafai duk da ya kasance yaro mai karancin shekaru amma ya tara ilimi mai tarin yawa.

A wata hira da Aminiya ta yi da shi, ya yin da labarunhausa na tattara bayyani cewa bayyana cewa ba ya wasa tare da yara masu makamancin shekarunsa saboda yadda ya kudirci zama babban malamin addinin musulunci.

Ya ce an haife shi ne a Zaria, Tudun wada, Sabon Layi a gidan Ali Mai Yasin kuma shekarunsa 8 a duniya. Ya yi karatu a Professors International Group of Schools, Zaria.

Yayin da aka tambaye shi yadda aka yi ya tara ilimi mai yawa, cewa ya yi:

Na yi karatu ne a wurin malamaina. Wanda kuma malamai ne da mahaifina ya zabo minsu kuma sun kasance suna mayar da hankali akan karatuna sosai saboda sun ga yanayin kokarina.

An kara da tambayarsa yana da shekaru nawa a duniya ya haddace Al’Qur’ani, inda ya bayar da amsa da:

Kamar yadda na ji labari cewa na haddace Al’Qur’ani ne tun lokacin ina da shekaru 3.”

An tambaye shi akan me zai ce akan wadanda suke ganin kamar magani aka ba shi har ya tara wannan ilimin, inda ya kada baki ya ce soyayyar manzon Allah ce ta sa har ya kai wannan matakin. Kuma yana karanta littafin Al-Burda wanda yake saukaka masa abubuwa.

Ya bayyana lokacin da ya fara tafsirin Qur’ani da kuma irin littafan da ya kasance yana nazari akansu, har ya ce:

Na fara tafsiri ne a shekarar 2021. Na kasance ina nazari a litattafai dayawa kafin in yi tafsiri. Amma dai daga cikinsu akwai su Jami’ul Ulumul Hikam wanda Imamu Kurtabi ya rubuta, shi ma tafsiri ne. Sannan da kuma Riyaduttafsir, na Sheikh Ibrahim Inyass. Da sauransu.”

Ya ce kuma matsawar mutum yana da mayar da hankali, komai kankantarsa zai gane karatu kuma ya iya abubuwan da ake tunanin dakyar ya iya yinsu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button