AddiniLabarai

Gaskiyar Labarin yadda yan ta’adda sunka taremu – Sheikh Ahmad Tijjani Guruntum

A yau ne labarin ya kewane kafafen sada zumunta na cewa yan ta’addan da ake tsammanin boko haram ko yan bindiga sunka tare ash sheikh Ahmed Tijjani Guruntum tare da tagawarsu wanda tabbas abun ya faru ga yadda abun ya faru daga bakin shehin malamin.

Kamar yadda yan uwa suka gani yanzu nan a shigowar a garin bauchi daga jamhuriyar Nijar saboda yadda abubu suka yadu a cikin al’umma wadansu hakane wadansu ba haka bane da kuma yadda wasu suke yada abubuwa masu tashin hankali wanda shima ya zama wajibi dole muyiwa yan uwa bayyani a taƙaice abinda ya faru abinda yake shine gaskiyar magana.

Kwanaki ukku da sunka wuce mun tafi jamhuriyar nijar domin gabatar da wasu darusa na addini so jiya munka kamala darusan da dare yau kuma cikin taimakon Allah muka fito gaskiya ne yan bidiga sun tare da safiyar yau so bayan fitowar mu muna kan hanya tare da sauran malamai da yanzu da muka tafi da su gaba daya , sai suka kewaye mu da bidigoginsu akan hanya sunka tsare mu, so lokacin da sunka tsare mu so abinda sunka fara yin kokarin yi a lokacin shine bude kofar motar.

So da yake central lock ne bazai buduba sai a cikin motar mu bude motar ko su bude mata wuta to bamu bude motar ba saboda duk mun dai dai ba zamu bude motar ba, so muna cikin wannan cece kuce daya daga cikin motocin da suke cikin tawagarmu ta baya malam sagir yana ciki, motar alhaji gwani to sai suka juya to daman duk kofar ragu ne sun so dukka motaocin su shigo ne, to ganin wacan motar zata juya sai kayi kanta da harbin bidiga cikin taimakon Allah juyawar ta sai direban mu ya hankalta da hankalinsu ya koma can shi kuma sai ya zaburi motar mu.

Cikin taimakon Allah dukka Allah ya kubutar da mu ba wadda aka ma rauni ba wadda akama kwarzane ba wanda wani abu ya same shi, akwai wasu bayin Allah wanda su ba a cikin tawagar mu suke ba to sai sunka shigo cikin attack din harbin ya same su ciki mutum biyu wanda labari ya iske mu ba wani rauni sunka ji ba.

Ga cikakken Bidiyon jawabin malam nan ku saurara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button