Kungiyar Izala Ta Kaddamar Da Katafaren Makaranta A Jihar Adamawa
Kungiyar Izala Ta Kaddamar Da Katafaren Makaranta A Jihar Adamawa
Daga Mahmud Isa Yola
Kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’ah Wa’ikamatis Sunnah ta bude sabon ginin katafaren makarantar Islamiya a Garin Dasin dake karamar hukumar Fufore, jihar Adamawa.
Makarantar mai suna Madarasatu Ta’alimil Qur’an Wasunnah daliban ta sun kasance suna karatu a cikin ajujuwan zana, wanda haka ya janyo hankalin kungiyar Izala ta kasa karkashin jagorancin kwamitin ilimi ta ware mukadan kudade saboda yiwa makarantar gini kayatacce, wanda ake budewa yau.
Shugaban kungiyar Izala na jihar Adamawa Alh Sahabo Magaji ne ya kaddamar da sabon ginin inda yace ilimi wani abu ne babba da kungiyar Izala ta saka a gaba. Yace burin kungiyar shine ta ilmantar da al’umma saboda a cewar shi, ilimi ne ke gyara al’umma.
Alh Sahabo wanda ya wakilci shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi kira ga mazauna yankin da su rike makarantar da hannu biyu, inda yace ta hakan ne zasu sakawa kungiya da ta gabatar musu da wannan aiki.
Shi ma a nashi jawabin kaddamarwar, mai jimillar garin Malam Shittu yayi godiya da katafaren ginin zamani da kungiyar tayi a yankin da yake shugabanta, inda ya kuma yi kira ga jama’ar sa da su kara kaimi wajen neman ilimi.
Sabon ginin makarantar ya kunshi ajujuwa, dakin ajiye littatafai (library) rijiyan burtsatsai (bore hole), bandaki na zamani, ofisoshin malamai, babban dakin taro da kuma farfajiyar haraba wanda aka shafe kasan shi da ‘interlock’.
Malam Isa Dasin, daya daga cikin malaman makarantar da ya gabatar da takadda mai taken tarihin makarantar yace yanzu haka suna da rijistan dalibai yara 420 da kuma dalibai matan Aure 370.
Shugaban kungiyar na karamar hukumar Fufure ne yayi jawabin godiya, inda ya jinjinawa kungiyar tun daga matakin kasa har zuwa jiha da karamar hukuma a bisa wanna gagarumar aiki. Shugaban ya kuma jinjina wa Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaba na kasa bisa tsayuwa da yayi na ganin an gabatar da wannan aiki.
Sources :rariya