Kannywood

Sarkin waka Nazir M Ahamd yayi Raddi Mai zafi kan Maganar wata jaruma da tace a daina haihuwa

Sarki Waka Nazir M Ahamd yayi raddi mai zafi kan maganar wata jarumar Kannywood tayi na cewa mutane su daina haihuwar yayanda basu iya kula da su.

Wanda wannan maganar da Jaruma Nafisa  Abdullahi tayi anyi ta cece kuce akanta a dandalin sada zumunta na  twitter inda shi kuma sarkin waka a yanzu nan ya fitar da magana mai zafin gaske wanda bai kira suna ba amma hausawa kance kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake ga abinda yake fadi.

Ba Almajirai Ne Yaran Da Iyayensu Suka Haifa Suka Kasa Kula Da Su Ba. Idan Kana Neman ‘Yayan Da Iyayensu Suka Kasa Kula Dasu, To Ka Taho Masana’antar Fim.”

Nan take mutane sun fara tofa albarkacin bakinsu akan wannan magana da sarkin waka yayi.

@Mustapha bin isah : Wannan gaskiya ne
@real_sarkinwaka
Allah yasa su gane suma sugyara har karsu.

@commissioner : Kunfi kusa, Bama Shiga Fadan Cikin gida, Dan in kana shiga fadan cikin gida wata rana zaka ji kunya, Kuje cen ku karata…

@gaskiya tsirara : Subhanallahi ranka ya dade cikin martabawa da nuna girma zakasa su fara gaya maka bakakyan maganganu ????

Sarkin waka ya ƙara da cewa sun san salon yaurdara da sherin da ake laƙawa sunan Almajiranci da iyayensu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button