Kannywood

Da Haihuwar Kilaki Da Almajiri wanne Yafi Alheri ? – Datti assalafy

A yau din nan sarkin waka yayi magana mai zafin gaske wanda ta shafe kafaffen sada zumunta inda shine datti assalafy shima ya tofa albarkacin bakinsu a shafinsa na mai suna arewa intelligence ga abinda yake cewa.

Naziru Sarkin Waka wanda asalinsa Almajiri ne ya saki zazzafan raddi ma wata gantalall!yar kila_ki ‘yar Hausa fim wacce a fakaice taci mutuncin Almajirai ma’abota Qur’ani

Ga raddin da Naziru Sarkin Waka ya mata kamar haka:
“Ba al’amajirai bane ‘ya’yan da iyayensu suka haifa suka kasa kula da su ba, idan kana neman ‘ya’yan da iyayensu suka haifa kuma suka kasa kula da su to ka taho masana’antar fim!” ~Naziru Sarkin Waka

Wannan raddin yayi daidai da abinda na fadi kwanaki, idan kana ganin cewa Datti Assalafiy ba dan fim bane, to ga Naziru nan a cikinsu yake, ya fimu sanin sirrinsu

Wannan shine tsantar gaskiya, kuma ko ba komai da ka haifi yarinyar da zata shiga sana’ar karuwanc! ta dinga yawo da gantali ana
kwanc!ya da ita a manyan hotel na cikin gida da kasashen waje, to yafi ma alheri ka haifi Almajiri wanda zaiyi ta gantali domin ya koyi Qur’ani

Mu a tsarin mu bama goyon baya bara, bara dabam yake da Almajiranci, to wakilan Yehodawa basa sukar bara kai tsaye, Almajiranci suke suka domin a hana karatun Qur’ani, ba zasuci nasara ba Insha Allah

Allah Ka taimaki Qur’ani da Ma’abota Qur’ani”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button