Kannywood

Har yanzu ba a dena yayinmu ba, Tsohuwar jarumar Kannywood – Farida Jalal

Advertisment

Tsohuwar jarumar Kannywood wacce ta dade a masana’antar inda ta kai fiye da shekaru 20 da suka gabata tana fim ta ce har yanzu ba a dena yayinsu ba.

A wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da ita a shirin Daga Bakin Mai Ita, ta fara da bayar da tarihinta inda ta ce an haifeta a garin Katsina inda ta tayi ta yi karatu.

Ta bayyana cewa ta wuce shekaru 20 a masana’antar kuma har yanzu haka akwai fina-finan da ta ke alfahari da su kwarai.

Ta ce da aka dena ganinta a fina-finai ba boyewa ta yi ba, ko yanzu idan aiki ya samu za su fita kuma za su yi.

Sai dai a cewarta, yanayin harkar ta su ne wasu suna tasowa ne yayin da wasu suke tafiya, don haka su sun tafi ne wasu kuma son zo suna taka rawarsu.

 

Sai dai a cewarta, yanayin harkar ta su ne wasu suna tasowa ne yayin da wasu suke tafiya, don haka su sun tafi ne wasu kuma son zo suna taka rawarsa,labarunhausaa na tattaro bayyanai

Yayin da aka yi mata tambaya idan an dena yayinsu ne, sai ta kada baki ta ce:

“A’a, ba za a ce an dena yayinmu ba gaskiya. Kusan in ce dalilin kuwa shi ne, mun dade a masana’antar. To ko ba komai dai in dai za a yi zancen masana’antar Kannywood, to za a sako mu a ciki.

“Ba za a ce an dena yayi ba. Har yanzu muna nan da masoyanmu, muna zumunci da su. Wasu ma har yanzu suna kallon irin gudunmawar da muka bayar a baya.”

Ta ce yanzu ta fi karkata ne akan sana’ar saye da siyarwa sai kuma yabon ma’aiki wanda ake gayyatarsu biki, suna ko kuma maulidi.

Ta ce babban abinda ya janyo hankalinta har ta fara fim a masana’antar Kannywood shi ne yadda ta ga jarumai suna fadakarwa.

Dangane da aure kuwa ta ce ta taba yi amma yanzu ba ta da aure. Ta haifi yara biyu, sai dai daya ya mutu saura daya.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button