Kannywood

Jarumi Lawan Ahmad Ya Sami Kyautar Sabuwar Mota.

Dan wasan fina-finan Hausa, Lawal Ahmad ya samu kyautar sabuwar Mota kirar Marsandi E320 a taron da jihar Katsina ta shirya domin karama jarumai yan asalin jihar.

Jihar Katsina a kowace shekara tana shirya taron karrama jarumai yan asalin jihar musamman wadanda suka nuna hazaka a fanni dabam dabam wanda ya hada da harkan kasuwanci, shakatawa da wasanni.

Da gidan Jaridar Premium Times ta tattauna da shi, Lawal Ahmad ya nuna farin cikin sa kan wannan karramawa da ya samu.

“ Ba’a taba yin irin wannan a Kannywood ba. Akan hada irin wadannan bukukuwa na karramawa amma sai dai a baka 
kwalin. Ita kuwa wannan Motace sukudun aka mika mini. Aiko kaga irin haka shine na farko a farfajiyar Kannywood.
“ saboda wannan karamci da na samu dama ina da mota da ni ke hawa kirar 406, zan ba matata ita ma ta hau.

KALLA CIKIN HOTO..


Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button