Labarai

ABIN TAKAICI: Wani Kwamishina a Neja ya yi wa matarsa kyautar bazata da wayar N400,000 (Kalli Hotuna)

Advertisment

Al’ummar jihar Neja sun bayyana fushi da takaicin su bayan wani faifan Bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta dake nuna Kwamishinan Kananan hukumomi da Masarautu na jihar, Abdul-Malik Sarkin Daji ya gabatar wa matar sa da kyautar waya kirar Iphone 11pro da ta kai darajar naira dubu N400,000 wanda ya yi daidai da dalar amurka ($999).

Mazauna jihar sun nuna takaicin su ainun, inda suka kira abin da Kwamishinan ya yi da almubazaranci da rashin tausayi yayin da tattalin arzikin jihar ke fuskantar barazana bisa annobar cutar COVID-19.

Kwamishinan ya yi amfani ne da kafafen sada zumunta wurin nuna wa duniya yadda ya taya matar sa murnar zagayowar haihuwar ta, inda ya shirya mata kayataccen bidiri tare da gabatar mata da kyautar bazata ta wayar zamani kirar Iphone 11pro.

Majiyar Hausa Daily Times ta jaridar “The Nation” ta turanci ta ruwaito al’ummar jihar sun yi ta bayyana ra’ayoyin su a kafafen Social Media game da wannan lamari, inda suka tuhume shi da karkatar da kaso ashirin (20%) na albashi da gwamnati ta yanke wa ma’aikata ya banzatar da su ga bukatun kansa a yayin da suka je iyalin su cikin mawuyacin hali.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button