Ɗan majalisar Najeriya na son a fara ɗaure ‘yan daudu ko tarar N500,000
Wani ƙudiri da aka gabatar a gaban Majalisar Wakilan Najeriya da ke son a yi wa Dokar Haramta Auren Jinsi a kwakwarima ya nemi a haramta daudu a ƙasar. BBCHausa na ruwaito


Da yake karanto sashe na 4 na dokar ranar Talata, ɗan majalisa mai wakiltar Toro daga Jihar Bauchi, Umar Muda Lawal, ya nemi a haramta daudu a fili ko kuma a ɓoye.
Ya nemi a saka ɗaurin wata shida a cikin dokar ko kuma tarar naira 500,000 ga duk wanda aka kama a matsayin ɗan daudu.
Ɗan majalisar na so a ƙara wani ƙaramin sashe na 4 cikin baka a cikin Dokar Haramta Auren Jinsi ta 2013 da zai ayyana cewa: “Duk wanda aka kama yana aikata daudu ya yi laifin da zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na wata shida ko kuma tarar N500,000.”
A jiya Talata ne ‘yan majalisar suka yi wa ƙudirin karatun farko. Sai sun yi karatu na biyu da na uku sannan ya zama doka.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



