Labarai

Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin rataya bisa kashe wani da ya ke zargi da soyayya da matarsa

A yau Litinin ne wata babbar kotu a Aiyetoro a Ogun ta yanke wa wani Adelake Bara hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin harbe wani Olaleye Oke da ya ke zargi da laifin yin lalata da ɗaya daga cikin matansa uku.jaridar DN na ruwaito

Kotun ta kama Bara da laifi guda ɗaya na kisan kai.

Da take yanke hukunci, Mai shari’a Patricia Oduniyi, ta bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi wa Bara ba tare da wata shakka ba.

Mai shari’a Oduniyi ya ce laifin ya ci karo da dokar manyan laifuka ta Ogun.

A yayin shari’ar, lauya mai shigar da kara ta jihar, Miss T.O Adeyemi, wacce babbar lauya ce a jihar, ta bayyana cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Mayu, 2018, da misalin ƙarfe 6 na yamma, a Afodan Farm Settlement, Ijoun, a unguwar Aiyetoro a Jihar Ogun.

Adeyemi ta ce marigayin yana gonarsa ne, sai Bara ya same shi ya zarge shi da soyayya da ɗaya daga cikin matansa.

Ta ƙara da cewa marigayin yana gonarsa ne, sai Bara ya same shi ya zarge shi da soyayya da daya daga cikin matansa.

“Bara wanda ke da mata uku ya fito da bindiga ya harbi Oke a kai, yayin da shi kuma ke ƙoƙarin bayyana cewa ba shi da wata alaka da wasu matan Bara da ake zargi,” inji ta.

Lauyan ta ce harbin da aka yi a kan Oke ne ya kai shi ga rasa ransa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button