Labarai

Soyayya Ruwan Zuma: Wani Saurayi Dan Shekara 25 zaiyi Wuff da Masoyiyarsa Mai Shekara 85

Wani dan kasar Kenya mai suna Muima, ya bayyana shirinsa na auren Thereza, mai shekaru 85.

A wani sabon faifan bidiyo da Afrimax English yayi a YouTube, masoyan sun bayyana labarin soyayya da yanke shawarar yin aure.

Shafin yanar gizo na Tuko ya ruwaito cewa, ma’auratan sun fara haduwa ne yayin da Muima da wasu abokansa ke neman gidan haya. Haka suka k’arasa gidanta tana yawan kiran Muima da “Mijina”.

Da yake magana game da rayuwarsa ta soyayya, Muima ya ce, “Wannan ita ce zabina, wannan ita ce farin cikina, kamar yadda kowa yake da nasa, kafin faranta wa wani rai, farantawa kanku rai, kada ku dogara ga ra’ayin wani.

“Yadda ta bi da ni (ni) ya sa na so ta kuma duk da cewa ita tsohuwa ce kuma a gaskiya, tana iya zama kakara amma ina sonta.”

Thereza, wadda kaka ce ta ce, “Ina da ‘ya’ya takwas da jikoki 20.

A cewarta “shekarun saurayina, zai iya zama na jikana na biyar. Yana so na kuma ina son shi. A shirye nake in sanya rigar aure da zobe.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button