Labarai

Fassarar Rubutun Professor Farouq Kperogy Mai Taken: “Dalilai 10 Cewar Osinbajo Zai Jawo Rikicin Addini” [A Nigeria, Idan Ya Zamo Shugaban Kasa]

Advertisment

Shugabancin Osinbajo tabbas zai sanya Nigeria cikin wutar da za ta yi saurin tarwatsa kasar. Wannan kuwa ba shaci-fadi ba ne, dalili ne akan sanannen abu gameda yadda Osinbajo ya tsani Musulmi da kuma kokarinsa na tabbatar da kungiyar Kiristoci ta RCCG ta mamaye shugabancin Nigeria.

Ga dalilai 10 na abinda na ke tsoro:
1. Wasikar kungiyar Kiristoci ta RCCG da ta bukaci dukkan Coci su bada goyon bayansu ga duk yayan kungiyar da ke neman kujerun siyasa ya samo asali ne daga Osinbajo, wanda tarihi ya tabbatar da yadda ya ke son sanya addini a siyasa.

Misali a shekarar 2013, ya kafa kungiya mai suna “Christian Conscience Group” (kungiyar wayar da kan Kiristoci) tareda Enoch Ajiboso, Dele Sobowale da kuma Rabaren Joseph Ajayi domin su tabbatar da an samu gwamna Kirista a jihar Lagos.

Kamar yadda jaridar Daily Post ta ranar 27 ga watan Satumba, 2013 ta ruwaito cewar wata kungiya ta ce: “Lokaci ya yi da Kirista zai mulki Lagos”. Wannan kungiyar tana karkashin jagorancin tsohon Atoni Janar kuma kwamishinan Shari’a ta jihar Lagos, wanda ya ke Fasto ne na Cocin RCCG, wato Farfesa Yemi Osinbajo. Kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Kamar yadda ya tabbatar da addinantar da siyasar 2023, a shekarar 2013 ya gabatar ta lacca mai taken “Kiristanci, Siyasa, a Yanzu da kuma Nan Gaba” wanda ya ingiza Kiristoci su tilastawa Tinubi ya amince da gwamna Kirista a Lagos a shekarar 2015 a bangaren Nigeria da ake cewa babu ruwan Yarbawa da bangarencin addini.
2. Duk da yadda Osinbajo ke yakin neman gwamna Kirista a Lagos, Musulmi bai taba yin gwamna a Ondo da Ekiti ba. A Ogun kuwa, inda nan ne tsatsonsa, Ibikunle Amosun shi ne kadai Musulmin da ya taba yin gwamna a jihar tun 1979 dukda cewar Musulmai sun kai kashi 50 cikin 100 na mutanen jihar, amma wannan daidai ne a wajen Osinbajo.
3. Hanyar da Osinbajo ya bi don fifita addini a Lagos kafin 2015, itace wanda ya ke amfani da ita yanzu. Wasikar RCCG kawai wani karamin bangare ne na wata manufa babba don amfani da addini.

Misali, a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2021 jaridar Guardian ta ruwaito Bishop Wale Oke, shugaban kungiyar Kiristocin Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) wanda Osinbajo memba ne, yana cewar; “Ba ma bukatar sake samun shiga Musu a 2023”.
A wani hira da aka yi da shi har yanzu a ranar 12 ga watan Fabrairu da ita Guardian din, Oke ya ce; “Bayan dole ne kudancin Nigeria ta samar da shugaban kasa na gaba, haka kuma shugaban kasar dole ya zamo Kirista, ban da Musulmi. Wannan abu ne mai muhimmanci”.
Haka a ranar 20 ga Fabrairu ta 2022, a wata lacca a Jos, kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito, shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN, Rabaren Samson Ayokunle ya ce dole Kiristoci su hada kansu domin zaban shugaban kasa Kirista. Ya fadi haka ne lokacin da ya ke gabatar da lacca mai taken; “Cin Nasara Akan Abokin Gabanka Ta Hanyar Hadin Kai” wanda hakan ya jawo a Kiristoci suka ji a zukatansu cewar Musulmai abokan gabarsu ne kuma dole a kadasu a 2023.

Shugaban Kiristocin ya ce: “A zaben da ya gabata, Buhari na da kuri’u kusan miliyan 14 wanda bai fi yawan kungiyar addini biyu a Nigeria ba, balle a yi maganar Kiristoci gaba dayansu. Idan muka hada kanmu, Ubangiji Ya san mutumin (da za mu zaba), mu ma mun san mutumin da Ubangiji ke son mu zaba. Munada shugabanci a CAN, idan muka saurari shugabanni, komai zai mana kyau”.
4. Osinbajo na da tsananin tsana wa Musulunci, amma ya lullube kansa da zakin baki. Yana mu’amala da Musulmai ne kawai saboda manufar siyasarsa.

Yadda Osinbajo ke kokarin Kiristantar da zaben 2023 ta kai ga sai da Bola Tinubu, wanda bai wani damuwa da addini ba ta sa a ranar 19 ga Maris ya nemi majalisar Koli ta Shari’a a Nigeria a Osogbo su kirkiri bangaren siyasa domin mara baya wa Musulmai da ke neman kujerun siyasa saboda sauran kungiyoyin addini sun fara wayar da kai wa mutanensu akan su goyo bayan nasu.
Ka kaddara abinda zai faru da Musulmai a arewa idan Osinbajo ya zamo shugaban kasa.
5. Osinbajo bai ganin Musulmi a matsayin dan kasa wanda ke da addini daban da nashi, yana ganin Musulmi ne a matsayin wanda ya halaka, wanda ke bukatar kebowa. Idan ba za’a iya kebosu ba kuwa, to a ciresu a harka kar a basu dama.

Misali, ranar 22 ga Fabrairu, jaridar Sunshine Truth ta jihar Ondo ta ruwaito yadda Osinbajo da gangan ya nuna farin cikinsa a fili don bakanta ran Musulmai a lokacin bikin bison Mama Muinat Mosekonla Mimiko, wacce ta bar Musulunci ta koma Kirista a karshen rayuwarta.
Da yawan Musulmai Yarbawa wadanda suka so ace ta daure akan Musulunci dukda yadda aka yita matsa mata ta bar Musulunci, sun ji bakin cikin izgilancin da Osinbajo ya musu na nuna farin cikinsa na cewar ta bar Musulunci a karshen rayuwarta.
Da ace Osinbajo kawai Fasto ne, da wannan babu matsala, amma a lokacin da ka ke shugaban kasa, ko mataimaki, matukar ka aikata haka to kana ingiza bangaranci ne cikin al’umma.

Ta kaddara ace Atiku Abubakar ya nuna farin cikinsa a wajen jana’izar wacce ta Musulunta a karshen rayuwarta ya nuna dadinsa na barinta Kiristanci zuwa Musulunci.
6. Musulmai Yarbawa suka ce akwai wata doka a kungiyar shari’a ta Osinbajo mai suna Simmons Cooper Partners cewar dole a tantance daukar Musulmi aiki a wajen, wanda hakan ya tabbatar da kashi 99 cikin dari na mutanen da ke aiki a gurin Kiristoci ne.
Kai, wani ma ya sirranta min cewar, akwai lokacin da Osinbajo ya gayawa wani ma’aikaci wanda ke da suna irinna Musulmai, amma Kirista ne, cewar idan har sunansa zai bashi matsala, to ya chanja sunan zuwa na Kiristoci.
7. Kungiyar Kiristoci ta Pentecostal na son Osinbajo ya zamo shugaban kasa saboda su ce abinda Fasto Enoch Adeboye ya fada ya zamo gaskiya na cewar yana son a rayuwarsa daya daga cikinsu ya zamo shugaban kasa.
Amma wannan na da hatsari sosai, domin sauran kungiyar Kiristoci da kuma Musulman arewa za su nemi fada da hakan. Idan wani Musulmi ya taso domin neman wata kujera don fada da waccar manufar, a lokacin rikicin addini na iya barkewa.

8. Bangarencin addini na Osinbajo ba abu ne da muka taba gani ba a Nigeria. Mafi yawan yan siyasa na amfani da addini ne don samun shugabanci, shi kuwa Osinbajo na son amfani da shugabanci ne don tabbatar da wani buri na addini.
9. A ranar 10 ga Nuwamba, 2019 a wata makala mai taken “Jarrabawar Da Ta Samu Dan’uwa Osinbajo”, a ciki marubucin jaridar Nigerian Tribune, Festus Adebayo ya bankado cewar, lokacin da Buhari bai da lafiya ya ke London, Osinbajo ya halarci wani addu’a na musamman na kungiyar Kiristocin RCCG a jiharsa ta Ogun, a gurin da Faston Cocin ya yi addu’ar Buhari ya mutu saboda Osinbajo ya zamo shugaban kasa a lokacin da shi Osinbajon ke cewa Amin da karfi.

Osinbajo ya firgita da bayyanan wannan abu, a lokacin da ya yi maza ya sa mai taimaka masa na musamman ya musa zargin.
Otto von Bismarck yana fadin cewar; “Kar ka taba gaskata abu a siyasa har sai an fito an karyata abin”. Abin mamaki, satin nan da ya gabata, wani abokina daga yankin Kudu maso Yamma ya ke tabbatar min da abin nan da ya faru.

10. Duk da yana aurar jikar Chief Obafemi Awolowo, har ma garinsu daya, amma Osinbajo bai dauko dabi’arsa ta cewar kar a gwama siyasa da addini ba.
A ranar 27 ga watan Janairu ta 1961, Awolowo ya gabatar da lacca mai taken “Siyasa da Addini”, wanda a ciki ya bada shawarar a daina addinantar da siyasa da kuma siyasantar da addini. Har ma yace; “Kungiyar addini kar ta taba zamowa mai magana da yawun masu neman mulki, idan kuma ta yi haka, to za ta nitse tareda wannan gwamnatin, sannan ba za’a sake iya fadan gaskiyar da ta sani ba”.
Bayan 2023, Osinbajo ya koma Cocinsa. Bai kamata ya zamo shugaban kasa mai yawan addinai da yawan al’adu kamar Nigeria ba.
Tsanar da Osinbajo ya yiwa Musulmi abin mamaki ne, domin a siyasance Musulmai ne suka kai shi inda ya ke a yanzu.
Prince Bola Ajibola wanda Musulmi ne mai kishi, shi ya fara kafa jami’ar Musulunci, shi ya fara nada Osinbajo a matsayin mai bashi shawara ta bangaren Shari’a a lokacin da yake Ministan Shari’a na kasa a lokacin mulkin IBB. Sannan ya sake kai Osinbajo Kotun Shari’a ta kasa da kasa.
Sannan Bola Tinubu shi ya bashi Kwamishinan Shari’a ta jihar Lagos wanda ya ke kokarin fada da Tinubu ta hanyar amfani da Kiristanci a matsayin makaminsa.
Tinubu shi ya gabatar da Osinbajo ga Buhari saboda ganin yadda ya ke son Fastoci (shi Buhari) saboda kokarinsa na kawar da cewar shi mai tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci ne, wanda hakan ta sa aka dauke shi a mataimakin shugaban kasa.
Yakin addini na da hatsari, kasashe kadan ne suka iya tsira. Kar kuce ban gargadeku ba.
.
Fassarawa: Abu Albani Auwal Ahmad

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

3 Comments

  1. Assalamu Alaikum gaskiya naji dadin wannan bayani naka Allah ya sa ya zama izinah ga al’ummarmu Allah Kuma yasa ya zama silar hadin kan Musulmai baki daya

  2. A GASKIA YAN NIGERIA WASU BASA DA HANKALI MAHAUKATA NE. WA YE BAYA MUTUWA YANXU A WANNAN MULKIN. WACE IRIN HAKIDA CE BAA NUNAWA. KO KUN DAUKI KIRISTA MUTUN NE A NIGERIA?. SAI TA DA TSAUNE TSAYE. DA KIRKIRAR KARYA DON A ZUB DA JINI. TUNA DA LAHIRA!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button