Abubuwa 18 da ake yi a lokacin aure da zasu iya kai masu yi gidan gyaran hali a jihar Kano – Abba Hikima
Lauya Abba Hikima yayi karin bayyani akan wata doka da anka shata a jiha kano ta hana kayan lefe to ba iya kawai lefe ta tsaya ba da abubuwa guda goma sha takwas 18 wanda yanzu haka gata a hannuna zan fadi sunan dokar.
Sunan wannan doka shine “doka wadda take haramta yin tsara be tsara ben aure a jihar kano” wannan shine sunan dokar a takaice.
Dalilin yin wannan Doka shine.
Domin an samu sauki wurin yin aure , da kuma yawan sake-saken aure anyi maganinsa, ba wai haka tace an haka kayan lefe haka kawai ba a’a akwai karin bayyani, sashi na biyar na wannan doka waɗannan abubuwan da za’a lissafo guda goma sha takwas 18 dukansu haramun ne a jihar kano yayin yin aure.
Abba hikima yace kafin ya karanto wadannan abubuwa zai fadi hukuncin su, hukuncin yin abu daya daga cikin wadannan abubuwa, zaman gidan yari na wata biyu ko tara ko kuma a hada mutum duka biyu, sashi na takwas na wannan doka ya fada hukunci wannan dokoki da aka kirkira.
Na farko : gaisuwar uwa da uba laifi ne.
Hukuncin sa wata biyu a gidan yari.
Na biyu: kudin zance laifi ne.
Hukuncin sa wata biyu a gidan yari.
Na ukku: Duk wanda yakai kayan lefe.
Hukuncin sa wata a gidan yari,ko wanda ya karba ko wanda ankayi da shi
Na Hudu: kayan biko laifi ne
Hukuncin sa wata biyu a gidan yari
Na biyar: kayan ada’a laifi ne
Na shidda: kuɗin aure doka ta soke shi
Na bakwai : kuɗin rigar mijin baya babu kyau.
Na takwas : kuɗin buɗa kai suma ba dai-dai bane.
Na tara: kudin ala budi doka ta soke
Na goma : kuɗin yan mata doka ta soke shi.
Na Sha daya : saye fura an soke shi
Na sha biyu: zaman ajo, doka ta haramta shi.
Na sha ukku: sayen baki
Na sha hudu: kudin kama hannu,
Na sha biyar gara aure ,
Na sha shidda: gara haihuwa .
Na sha bakwai: yin biki
Na sha takwas : kayan ɓuda kai.
Laifi ne duk wanda yayi shi zai iya tafiya gidan yari domin girba abinda ya shukka.
Yan sanda suna da damar kama duk wanda yayi wannan abu domin “police act” ya fadi duk abinda yake laifi a kasa , a tara a jiha ko a karamar hukuma dan sanda na da damar kama duk wanda yayi wannan laifi.
Ga bidiyon nan ku saurara domin jin cikakken bayani.