Labarai

Yansanda Sun Kama Wani Tsoho Mai Shekaru 60 Da Laifin Sha Da Sayar Da Miyagun Kwayoyi

Advertisment

Rundunar Yan sandan jahar Katsina ta kama wani dattijo mai shekaru 60 mai suna Ilyasu Abdullahi da zargin sha da kuma sayar da miyagun Kwayoyi a Katsina.Yansanda Sun Kama Wani Tsoho Mai Shekaru 60 Da Laifin Sha Da Sayar Da Miyagun Kwayoyi
Dattijon a yayin da kakakin rundunar Yan sandan jahar SP Gambo Isah ya ke tambayarshi akan abinda ake tuhumuarsa da shi, ya amsa laifinsa Jakadiya tv sun bayyana bidiyon hirarsa da jami’an tsaro nayi.
Ga bidiyon nan.

Abdullahi wanda ya je gidan yari kusan sau 4 da kuma zuwa hannaun jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi, NDLEA kimanin sau 10, ya ce in Allah ya yarda daga yanzu ya daina ta’ammali da miyagun Kwayoyi.
A halin da ake yanzu haka wasu daga cikin yayanshi na cikinsa suna shan kwayoyin kamar yadda ya ce.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button