Labarin mijin da yake zargin matarsa,da anka bayyana abun da take sai da hankalin kowa ya tashi


As sheikh Aminu Daurawa ya kawo wani labarin wani rikici da ya faru tsakamin mata da miji wanda yaga yanayin rayuwar ta ya canza wanda har ya fara kai karar ta inda mahaifiyarta yace shifa bai gamsu da yadda take gudanar da rayuwar ta ba yana gajin canje canje da yawa.
Sai uwa ta fara fada tana fadin ana son a ɓatawa ‘yar ta suna ita tayiwa yarta tarbiyya saboda haka idan sharri za’a yi mata a rabu kawai yace a’a ba maganar rabuwa, sai sunka je wajen malam a hukumar hisbah kenan wajen neman shawara.
Ash Sheikh Daurawa yace ta nan mun kayi amfani da kwararru wajen bibiyar waya da shafu da yanar gizo da ake amfani da su.
Munka karbi numbobinta munkayi amfani da kwararru a wannan fage muka nema hurumin kotu domin bada damar bibiyar wayoyinta, wato da munka baiwa waɗannan kwararru aiki sai sunka ce a basu wata guda.
Bayan wata guda sai sunka zo mana da lapton a ciki, wato da anka zo da lapton din babar yarinya ta gefe zaune , mijinta yana gefe, ita yarinyar tana gefe , muma jami’an hisbah muna zaune, sai sunka ce ta ina za’a fara?
Na farko tace tana da layi daya, amma layi hudu take da shi kowane layi sai da anka fadi numbersa, tana amfani da waya daya amma wayoyinta ukku, duk wani sautin murya da anka turo ko video ko hoto sai da ankayi downloading dinsu.
Ashe akwai wani kawali wanda yake birnin tarayya Abuja shi kuma yana amfani da nasa na jahohi waɗanda suke bibiyar yan mata ko suna da aure ko zawarawa masu wannan ɓangaren suke bukata ta yadda za’a nemo musu su yaudare su, su dau hankali su, su raba su da aurensu aje ayi lalata da su a dawo gida batare da kowa yasani ba sai Allah.
Matarsa ta taɓa tafiya sati biyu a tafiyar ance taje umrah Saudiyya amma kuma bata shiga Saudiyya ba,amma a cikin passport dinta an buga visa, a passport dinta an buga tambarin immigration ta fita Nijeriya , a passport dinta an buga tambarin immigration na Saudiyya ta sauka Saudiyya.
A Saudiyya an buga tambarin alfuruj tambarin ta fito rana kaza daga Saudiya, immigration ta buga tambarin ta sauka daga Nijeriya , amma ba inda taje.
Kuma duk zagayen da tayi babu inda ta shiga jirgin sai daga nan zuwa abuja saboda haka sati biyu a cikin gidan wani manyan kasa nan tayi, kuma anka dawo da ita gidan mijinta harda guruji ta dawo daga umrah kuma duk karya ne.
Wato da anka fara zazagu abubuwan nan sai da munka fara gumi bayan ga Ac ga fanka, sai uwarta tayi shiru kamar ruwa sun cita.
Wannan shine bidiyon labarin da malam yake bayarwa.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




