Labarai

(Bidiyo)Wani magidanci ya jefa mahaifyar ramin kwata Saboda bata da lafiya matar sa bazata iya jiyya ba

Wannan labari akwai matukar ban tsoro a cikinsa duba da ace mutum mahaifiyarsa ba lafiya yaga dawainiya da ita rashin imani da rashin tausayi yayi yawa.

A wajen majalisin karatu Mallam ya bada labarin cewa akwai wata mata da tazo tana bashi labarin cewa:

Akwai wani makwabcinsu da mahaifiyar babu lafiya tana kauye sai ya daukota yakai asibiti da ta samu sauki sai ya kawota a gidansa domin kulawa da ita

A nan fa matarsa tace ita kam bazata iya jinyar uwar wani ba tunda ba mahaifiyar ta bace.

Tace yanzu kam sai da a zabi daya ko a mayar da ita asibiti daga nan dai ko allura ayi mata su huta dan yanzu bata da wani amfanin da za’a cewa a barta.

ko kuma ya dauketa ya maida ta kauye inda ya daukota amma ita wallahi bazata rike uwar wani ba akai akai har ya gamsu shima bai yarda a rike uwarsa ba.
Ranar da dare sai yaje yace mama likita yace a mayar da ke asibiti tace to a bari na kimtso, ta kimtsa ta fito sai aka sanyata mota sai yaje wani wuri yace mama sauko an kawo.

Sai ya kama hannunta kamar za’a tsallaka wata kwalbati tana daga kafa zata tsalakawa sai ya sake ta ta zunduma cikin kwalbatin nan.

Sai wani ya fito sallah asubah ya kama jin nishi a cikin kwalbati ya dawo gida ya rufe yace a zamanin nan baka zuwa waje sai ka kira mutane.

Sai yaje ya gawa mutane cewa yanajin nishin a cikin kwata kusa ga gidanka, koda anka duba sai anga ka tsohuwa cikin kwata tasha ruwan kwata sai anka fitar da ita”.

Ga Bidiyon nan kasa ku saurara kuji yadda mama ta bada bayyanin yadda ɗanta ya kawota nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button