Rashin Tsaro: Masari ya yi sabuwar dokar hana dabancin siyasa da manna fastoci a ko ina


Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya rattaba hannu a wata sabuwar doka a yunƙurin sa na magance rashin tsaro a jihar.
Yahaya Sirika, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, shi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a Katsina.
Daily Nigerian ruwaito sirika ya yi bayanin cewa gwamnan ya yi amfani ne da sashi na 176(2) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999 da ya baiwa gwamnan jiha ikon yin doka a kan kansa.
A cewar sa, dokar, wacce ta fara aiki tun 1 ga watan Janairu, ta yamma dukkanin wani nau’i na dabancin siyasa da aikata wasu Laifuka makamantan hakan.
Kwamishinan ya ƙara da cewa dokar ta kuma hana manna fastocin siyasa a rawul-rawul, gine-ginen gwamnati, ofisoshi da sauran guraren jama’a a jihar.
Ya ce dokar ta hana duk wani taro na ƴan baranda siyasa da su ka haɗa da Bacha, Ƙauraye, koma wanne irin suna a ke kiransu, da zai razana al’umma a jihar.
Sirika ya yi gargaɗi cewa duk wanda ya saɓa dokar za a kama da kaifin karya sashe na 114 na dokar ‘penal code’ ta jihar.



