Labarai

Yan sanda sun gurfanar da yara yan shekara 6, da masu shekara 9 a gaban Kotu

Alkalin Kotun Sharia ta 1 da ke garin Birnin kebbi ya ba da belin wasu yara guda biyar masu shekara 6 zuwa 9 bayan an gurfanar da su a gaban Kotu bisa zargin sace wayar lantarki. Yaran sun musanta wannan zargi.
Yaran Yan makaranta Nursery da Primary be kamar yadda Lauyan iyayen yaran ya ambata,jaridar isyaku na ruwaito

Mun samo cewa wani Safeton Yan sanda mai sun Iliyasa Alhassan wanda ke ofishin Yan sanda na garin Kamba ne ya yi karar yaran bisa zargin sace masa wayar wutar lantarki na gida da yake ginawa.

Wata majiya ta ce zancen ya kai kusan wata biyu ana yinsa wanda ya samo asali daga ofishin Yan sanda na garin Kamba, zuwa ofishin Yan sanda na gundumar Bunza (Police area command) har zuwa sashen binciken manyan laifuka na CID a Shelkwatar Yan sanda na jihar Kebbi da ke garin Birnin kebbi, kafin daga bisani aka gurfanar da yaran a gaban Kotu.

Mun samo cewa hatta tsare yaran an yi lokacin bincike, na tsawon kwana biyu da wuni daya, kuma aka sake tsare su na tsawo kwana daya da wuni daya yayin gudanar da bincike.

Kotu ta dage ci gaba da sauraron shari’ar har ranar 9 ga watan Mayu 2022. Kotu ta kuma bayar da belin yaran har zuwa wannan ranar.

Ga bayyanin yaran da layan da ke karesu nan ku saurara

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button