Babu Masu Adawa Da Rundinar Sars Sai ‘Yan Ta’adda Da Wakilansu ~ Datti Assalafy
Cikin kwanakin nan mutanen kudu da maso yammaci da babban birnin tarayya Abuja suna jagorantar zanga-zanga da kira ga gwamnatin shugaba Buhari a kan cewa lallai sai an rushe rundinar ‘Yan sanda masu yaki da ‘yan fashi da makami da sauran masu aikata miyagun laifuka, wato Special Anti-Robbery Squad (SARS)
Masu zanga-zangar sunyi take da #ENDSARSNOW, saboda abinda suke zargi na cewa rundinar SARS tana kisan mutane haka siddan, da karban cin hanci da rashawa, don haka suke kira da a rushe rundinar SARS din gabaki daya
Shekaru kusan 30 da aka kafa rundinar SARS a birnin Lagos, lokacin da ta’addancin barayi da ‘yan fashi ya munana matuka har suke iya fitowa cikin gari da rana tsaka suna kashe mutane suna kwace dukiya, abinda SARS suke yaki dashi kenan har zuwa yau, lallai a rundinar ‘Yan sandan Nigeria babu wata rundina da take zama babban barazana ga barayi da ‘yan ta’adda kamar SARS, hatta barayi sun gwammace su shiga hannun sojoji madadin su shiga hannun SARS
Kwanannan kwamandan rundinar Federal SARS na FCT Abuja Command, DSP Ahmed Mustapha ya kama wani rikakken kwamandan yakin Boko Haram a birnin tarayya Abuja, haka yayi ta kamasu a gewayen Abuja da Nasarawa
Ayyukan SARS bai takaita ga yaki da barayi ba, suna yaki da ‘yan kungiyar asiri masu shan jini da sarrafa naman mutane, suna yaki da barayin yanar gizo masu damfarar mutane kudi, suna yaki da masu garkuwa da mutane da kuma kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da Ansaru da manyan barayin daji
Nigeria tana cikin wannan halin ana aikata manyan miyagun laifuka ko ta ina, duk da karancin jami’an tsaron da karancin kwararru da ake da shi sai muka wayi gari wasu munafukai ‘ya’yan asara ‘yan kwangila wakilan kungiyoyin ta’addanci da na manyan barayi sun karbo kwangilar kira ga gwamnatin Nigeria da a rushe rundinar SARS saboda tsantsar makirci
Wallahi wannan babban makirci ne aka tsara game da makomar tsaron Nigeria, duk mai hankali da tunani da hangen nesa yasan cewa masu wannan kiran saka su aka yi, kuma manufar shine a karya lagon tsaron da ake kokarin samarwa a musamman a Arewa, makarkashiya aka shirya wa Arewa, amma sai aka faro kwangilar daga kudu, Alhamdulillah ‘yan Arewa basu nuna goyon baya ba, sai wawaye kalilan a dandalin Twitter da Facebook
Dukkan jami’an tsaro ba’a rasa kura-kurai a cikin aikin su, hakanan baragurbi, laifin mutane kalilan bai kamata ace ya shafi kowa da kowa ba, maimakon kira da a rushe rundinar SARS mai zaisa ba zasu ce ayi garambawul a gyara rundinar SARS ba?, kokarin SARS din suke yaka, saboda SARS ta zama babban tarnaki ga manyan barayin zamani da masu gidansu wadanda suke daukar nauyin ta’addanci
Wallahi duk wanda ya san sha’anin tsaro zai bada bayani na cikakken goyon baya game da ayyukan da SARS suke yi a yankin Arewa da kudancin Kasar, mun san kokari da SARS sukeyi yanzu haka a bangaren yaki da Boko Haram da masu garkuwa da mutane, mun san yadda suke sadaukar da rayuwarsu a cikin tsananin duhun dare, zafin rana da ruwan sama, suna shiga kowani lungu da sako da manyan dazuka da tsaunuka farautar miyagun mutane, don haka sam SARS basu cancanci wannan sakamakon ba
Kira a rushe SARS kwangila ne daga gurin makiya zaman lafiyar Nigeria, wasu wawayen cikinmu kuma daga nan Arewa suna ta taya su, basu san mu ake so a yaka ba, kuma ba su san inda aka dosa ba, wannan zanga zangar da ake yi akan wai a kawo karshen SARS ni na dauki zanga zangar a matsayin taron wawaye, taron ‘yan iska, kuma taron wakilan tsageru, ‘yan fashi da makami da kuma wakilan masu garkuwa da mutane
Wani abin takaici da abin haushi ma wai har da wasu manyan mu na Arewa suna goyon bayan wannan shirmen, ba dan komai ba sai dan kawai suna adawa da gwamnatin Baba Buhari, don haka suke goyon bayan duk wani abinda aka kira da zanga zanga, ko da kuwa abin zai cutar da Arewa babu ruwan su, burin su kawai ace shugaba Muhammadu Buhari ya gaza bai iya ba to sunyi nasara a ganin su, Alhamdulillah Shugaba Buhari da shugaban majalisar Dattawa da shugaban ‘yan ssandana kasa IGP Muhammad Abubakar Adamu basu goyi bayan wannan shirmen ba
Muna kira ga rundinar ‘yan sandan Nigeria Nigeria Police Force da gwamnatin shugaba Buhari da ta karawa rundinar SARS karfin iko, a wadatasu da kayan aiki irin na zamani, sannan a tsarkake batagarin cikinsu
Muna kira da asa ido akan jami’an tsaron da suke cin zarafin mutane, masu cin zarafin mutane kuma ba Police ko SARS bane kadai, akwai a cikin sojoji, Custom, Air Force, DSS da sauran su.
Dan haka muyi hankali jama’ar Arewa, kun taba ganin masu shirya zanga-zangar rushe SARS sun shirya zanga-zangar a rushe Boko Haram? ba damuwarsu Boko Haram, saboda bai shafesu ba, ana so a ruguza mu ne, bayan kokarin da shugaba Buhari ke yi akan tsaron Nigeria
Yaa Allah Ka taimaki rundinar SARS da gwamnatin shugaba Buhari, Ka shiryar da batagarin cikinsu, Ka basu cikakken nasara akan miyagun mutane Amin


